Gidan adana kayayyakin tarihin yankin Asiya na Smithsonian, ya mayar da kashi na 2 da na 3 na rubuce rubucen hannu da aka yi kan siliki na Zidanku, na lokacin yake-yake a kasar Sin, ga hukumar kula da al’adun gargajiya da aka gada ta kasar.
An yi bikin mika rubuce-rubucen ne jiya Juma’a, a ofishin jakadancin Sin dake birnin Washington na Amurka.
- Mutum 3 Sun Rasu, Wasu Sun Jikkata Yayin Da Bama-bamai Suka Tashi A Hanyar Borno
- Gwamnatin Tarayya Na Ƙoƙarin Farfaɗo Da Sashin Raba Wutar Lantarki A Nijeriya
A shekarar 1946 ne aka tafi da rubuce-rubucen wanda aka tono a shekarar 1942 daga wurin tarihi na Zidanku dake lardin Hunan, zuwa Amurka ba bisa ka’ida ba.
Rubuce-rubucen na Zidanku wanda aka yi a kan siliki, sun kasu zuwa kashi 3. Na 2 shi ne Wuxing Ling sai Gongshou Zhan na 3.
A matsayinsu na rubuce-rubucen hannu daya tilo na lokacin yake-yake da aka tono a kasar Sin, rubuce-rubucen da aka yi kan siliki na Zidanku, mai shekaru sama da 2000, su ne irinsu na farko da aka gano, wadanda ke wakiltar misalin ainihin littafin Sinanci na zamanin da. Yana da muhimmanci a matsayin tubalin nazarin rubutun Sinanci da adabi, da ma tarihin koyar da Sinanci da kwarewa a harshen.
Cikin jawabin da ya gabatar ta bidiyo, mataimakin ministan kula da al’adu da yawon bude ido na kasar Sin Rao Quan, ya ce dawowar rubuce-rubucen na Wuxing Ling da Gongshou Zhan, na tabbatar da cewa za a iya nazarta da kare wadannan kayayyakin gargajiya masu daraja yadda ya kamata a mahaifarsu. (Fa’iza)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp