Hukumar Kula da Gidan Talabijin na Abubakar Rimi (ARTV) mallakin jihar Kano ta karyata zargin cin hanci da wariya da ake yi wa shugabanta, Mustapha Indabawa, inda ta ce, rikicin da ke faruwa a gidan talabijin din, jam’iyyar adawa ta APC ce ta shirya shi.
Jaridar national daily ta rahoto cewa, Hukumar jin Korafe-korafen Jama’a da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano na binciken manajan daraktan gidan talabijin na ARTV kan zargin almubazzaranci da kuma cin zarafin aiki.
- Ƙungiyar Ɗalibai Ta Yi Barazanar Zanga-zanga Saboda Ƙarancin Man Fetur
- ‘Yansanda Sun Gurfanar Da ‘Yan Daba 104 A Kano
Binciken ya biyo bayan wani korafi na hadin gwiwa da kungiyoyin yada labarai da suka hada kungiyar ‘yan jarida ta Nijeriya (NUJ) da kungiyar gidajen talabijin da rediyo (RATTAWU) suka kai wa gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf kan zargin karkatar da wasu kudade da suka kai kimanin Naira miliyan 100 da kuma cin zarafin aiki.
In ba a manta ba dai, Indabawa na cikin sabbin shugabannin ma’aikatan da gwamna Yusuf ya nada a watannin baya.
Sai dai, gidan talabijin din ya musanta zargin, yana mai cewa, wasu ne daga waje da hadin gwiwar na cikin gida ne suke kokarin tayar da rikici a gidan talabijin din na ARTV.