Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a yayin taron manema labarai na yau da kullum Larabar nan cewa, a tsawon shekaru, Amurka ta kafa gidajen yari ba bisa ka’ida ba a kasashe da yankuna a kalla 54, inda take tsare wadanda wai ake zargi da aikata ta’addanci a asirce ba bisa ka’ida ba, tare da azabtar da su don su bayyana abubuwan da ba haka ba ne. Gidan yarin Guantanamo yana daya daga cikin su. Kuma wannan misali ne na take hakkin doka da ‘yancin dan Adam a kasar Amurka.
Rahotanni sun bayyana cewa, a baya-bayan nan, wakilan musamman na MDD, sun bayyana bayan da suka ziyarci gidan yarin na Guantanamo cewa, har yanzu Amurka na ci gaba da musgunawa fursunoni, kuma ya kamata gwamnatin Amurka ta dauki nauyin abin da ta aikata, tare da ba da hakuri, da ceto da kuma biyan diyya ga wadanda abin ya shafa. (Mai fassarawa: Ibrahim)