Gidauniyar Zahra Relief Foundation ta aike da saƙon ta’aziyya da jaje ga waɗanda hatsarin tankar gas da ya rutsa da su a babbar hanyar Karu da ke Abuja a daren ranar Laraba.
Wannan hatsari ya jawo asarar rayuka da dukiyoyi, yayin da mutane da dama suka jikkata.
- Xi Ya Bukaci A Bude Sabbin Hanyoyin Samun Ci Gaba Yayin Rangadinsa A Lardin Yunnan
- Mun Yi Watsi Da Ayyana Dokar Ta-Ɓaci Da Tinubu Ya Yi A Ribas – Shugabannin Adawa
A saƙon jaje da gidauniyar ta fitar, ta bayyana alhininta kan wannan mummunan lamari tare da jajanta wa iyalai, ‘yan uwa, da duk wanda abin ya rutsa da su.
Gidauniyar Zahra Relief Foundation ta buƙaci al’umma da su taimaka ta hanyoyin da za su iya domin rage raɗaɗin da iftila’in ya haifar.
Ta kuma jaddada buƙatar bayar da tallafin jini ga waɗanda suka jikkata, inda ta bayyana cewa hakan yana daga cikin koyarwar addinin Musulunci na taimakon juna da ceton rayuka.
Rahotanni sun nuna cewa akwai asibitoci da ake iya bayar da gudunmawar jini ga waɗanda suka samu raunuka a hatsarin, waɗanda suka haɗa da National Hospital Abuja da Karu General Hospital.
Haka kuma, an buƙaci duk wanda ke da buƙatar ƙarin bayani ko kuma yake son bayar da gudunmawa ya tuntuɓi Hukumar Bayar da Jini ta Ƙasa a lambar waya 07088370905 ko ya bi duk wata hanya da za ta kai ga hakan.
A ƙarshe, gidauniyar ta roƙi Allah Maɗaukakin Sarki da ya bai wa waɗanda suka jikkata lafiya, ya mayar da alheri ga waɗanda suka yi asara, kuma ya kiyaye aukuwar irin wannan iftila’i a gaba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp