A kalla yara dari hudu, marayu da masu karamin karfi daga kananan hukumomi shida na jihar Kebbi ne suka samu tallafin karatu daga Gidauniyar M-TECH, ta hanyar ba su fom din JAMB kyauta tare da biyan dukkan kudaden karatu ga wadanda suka ci jarabawar tantancewar da aka gudanar a dukkan jami’o’in ko kuma kwalejin da ke fadin jahohin kasar nan.
Shugaban Gidauniyar M-TECH, Alhaji Manir Musa Jega, ya bayyana cewa an zabo matasa marasa galihu ne bisa aikin tantancewa da aka yi da nufin samun mabukata na gaskiya ko kuma marasa galihu su iya samun wannan tallafin karatu a kyauta da gidaumiyata ta M-TECH ke bayarwa.
- Alamomin Cutar Shan Inna Sun Bulla A Kananan Hukumomi 9 Na Jihar Kebbi
- Gwamnatin Kebbi Ta Kaddamar da Aikin Gina Tashar Motoci Ta Zamani A Birnin Kebbi
Kazalika, ya kara da cewa” Gidauniyar na ba su fom din JAMB kyauta da guraben karo ilimi amma ba su da mai taimaka musu da kudi don ci gaba da karatunsu a manyan makarantun da ke fadin jihohin kasar nan. Bisa ga hakan ne gidauniyar M-TECH ke taimakawa don ganin cewa ‘ya’yan marasa galihu ko marayu sun ci gaba da kararunsu a manyan makarantun kasar nan, inji Injiniya Manir Jega”.
Ya ce “mutanen da aka zabo sun fito ne daga kananan hukumomi shida na jihar da suka ci gajiyar tallafin, kuma sun hada da kanana hukumomin Birnin Kebbi da Jega da Bunza da Maiyama da Aliero da Gwandu. Haka kuma an gudanar da wata jarrabawar tantancewa don a zaɓi mafi kyawun su, inji Shugaban gidauniyar M-TECH Injiniya Manir Jega”.
A cewarsa, don karfafa musu gwiwa ne ta hanyar ba su tallafin karatu kuma gidauniyata ta M-TECH ta kafa cibiyar mock ta UTME domin sanar da su dabarun na’ura mai kwakwalwa domin samun nasarar rubuta jarabawar ta kwamfuta. Ya kara da cewa wadanda suka yi nasara za a biya musu kudaden tallafin karatu a cikin manyan makarantun da suka zaba na jahohin kasar Nijeriya.
Har ilayau, Injiniya Manir Jega yana kira ga masu hannu da shuni a cikin al’umma da su taimaka wa masu karamin karfi da wadanda suke da kuduri aniyar yin karatu amma iyayensu ba sa raye ko kuma ba su da karfin kudi don daukar nauyin karatun su.
Ya kuma yabawa Gwamnan jihar Kebbi, Kwamared Dakta Nasir Idris bisa yadda ya zuba jari sosai a fannin ilimi a cikin watanni takwas kacal a kan karagar mulki da ma sauran sassan don ci gaban al’ummar jihar.
Ya kuma yi kira ga al’umma a fadin jihar da su ci gaba da baiwa gwamnati mai ci yanzu goyon baya da nufin samun rabon dimokuradiyya tare da yin addu’o’in samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar da kasa baki daya.