Gidauniyar Sam Nda-Isaiah, ta gabatar da cakin Naira miliyan 250 da Gwamnan Jihar Neja Mohammed Umar Bago, ya bayar domin bai wa direban Adaidaita Sahu, Auwalu Salisu, mazaunin Kano, da ya zama gwarzon matashin kamfanin “LEADERSHIP” na shekarar 2023 bayan tsintar Naira miliyan 15 a babur dinsa kuma mayar ga masu shi.
Babban Editan Jaridar “LEADERSHIP”, Mista Azu Ishiekwene, wanda kuma darakta ne a gidauniyar Sam Nda-Isaiah, shi ya miƙa wa Salisu caki a shalkwatar Kamfanin, bisa shaidawar kawun Salisu, Abba Tukur, da kuma Babban Manajan Gidan Rediyo Arewa, Shehu Bala Kabara.
Bayan ya miƙa wa Salisu cakin, Ishiekwene ya bayyana godiya ga Gwamna Bago, bisa wannan gudummawar da ya bayar tare da yaba wa wanda ya karɓi cakin na nuna irin wannan abin ban mamaki ta ɗabi’ar gaskiya tare da shawartarsa na ya yi amfani da kuɗaɗen ta hanyar da ta dace.
Cikin jawabinsa a madadin Salisu, Kabara ya jinjina wa kamfanin LEADERSHIP na karramawar da gudunmawar Gwamna Bago, inda ya yi alƙawarin za a yi amfani da kudaden ta hanyar da ya kamata.
Gwamna Bago, ya yi wa Salisu, alƙawarin kyautar Naira miliyan 250 a madadin Shugaba Tinubu da muƙarrabansa da Ƙungiyar Gwamnonin APC, yayin taron shekara-shekara na kamfanin LEADERSHIP.
Daga baya aka gabatar da Salisu a matsayin gwarzon matashin kamfanin jaridar na 2023 saboda halin gaskiyarsa, gwamnan ya cika alkawarin da ya yi wa Salisu ta hannun Gidauniyar Sam Nda-Isaiah.
Matashin Salisu ya kuma samu tallafin karatu a Jami’ar Baze da ke birnin tarayya Abuja, har zuwa matakin digirin digirgir, daga ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party a zaɓen 2023, Peter Obi.