Wani gini mai hawa biyu da ake tsaka da aikinsa, ya rufta a garin Fatakwal da ke Jihar Ribas.
Ginin wanda ya rufta a yau Alhamis, yana yankin Ada George da ke a garin na Fatakwal.
- Zaman Lafiya Zai Bunkasa A Kaduna -Uba Sani
- Kungiyar Musulmi Ta Kasar Sin Ta Gudanar Da Liyafar Bikin Babbar Sallah
Wasu mazauna garin da abin ya auku a gabansu, sun dora laifin ruftawar ginin, kan rashin yin amfani da ingantattun kayan aiki.
Wani ganau ya bayyana cewa, babu wanda ya rasa ransa, inda ya kara da cewa, sai dai mutum uku da ruftawar ginin ta rutsa da su sun samu raunuka amma an ceto su.
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, SP Grace Iringe Koko, ba ta fitar da wata sanarwa kan aukuwar lamarin ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp