Wani gidan ƙasa ya rushe a ranar Lahadi a ƙauyen Kabak, ƙaramar hukumar Kirikasamma a Jihar Jigawa, inda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum ɗaya tare da jikkata wasu mutane bakwai bayan saukar ruwan sama mai ƙarfi..
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, SP Shisu Lawal, ya ce an garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa Asibitin Gwamnati na Kirikasamma.
- Kasar Sin Ta Zama Wurin Da Aka Fi Zaba Domin Warware Takaddamar Cinikayya Da Ta Shafi Kasa Da Kasa
- An Kama Mutane 30 Da Zargin Laifin Aikin Dabanci A Yayin Zagayen Maulidi A Neja
Ya ƙara da cewa shugaban ƙaramar hukumar, Hon. Marma, ya ziyarci waɗanda abin ya shafa tare da bayar da tallafin Naira 500,000 domin kula da marasa lafiya da kuma Naira 100,000 ga iyalan mamacin.
A cewar jami’an ƙaramar hukumar, an sallami mutane biyu daga cikin waɗanda suka jikkata daga asibiti.
Haka kuma shugaban ƙaramar hukumar ya kai ziyara ta’aziyya ga iyalan wanda ya rasu.
Hukumomi sun shawarci jama’a su tabbatar da cewa gidajensu suna da tsaro da karko, tare da kaucewa gina gidaje a kan magudanan ruwa a wannan lokacin na damina.
Hukumar Hasashen Yanayi ta Nijeriya (NiMet) ta yi gargaÉ—in cewa Kirikasamma na daga cikin wuraren da za a iya fuskantar ambaliyar ruwa a bana.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp