• English
  • Business News
Tuesday, November 4, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ginin Hedkwatar Ecowas: Al’ummar Afrika Ba Za Su Taba Mantawa Da Tallafin Kasar Sin Ba

by CMG Hausa
3 years ago
ECOWAS

Tasiri da taimakon kasar Sin ga nahiyar Afrika kawo yanzu, abubuwa ne da ba za su iya misaltuwa ko bayyanuwa ba, saboda yawansu da kuma karfi da moriyar da suke samarwa. 

A farkon makon nan ne aka aza tubalin ginin hedkwatar kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika (ECOWAS), a Abuja, babban birnin Nijeriya. Inda ya kasance wani katafaren aiki, kuma babbar nasara ga kungiyar ta ECOWAS, domin a karon farko, muhimman sassanta uku, wato kotun kungiyar da majalisar dokoki da sakatariyarta, za su kasance a dunkule, karkashin inuwa guda maimakon yadda suke a mabambantan wurare.

  • Rukunoni Biyu Na ‘Yan Sama Jannatin Kasar Sin Sun Yi Musayar Aiki A Tashar Binciken Samaniya Ta Sin

Hakika, taimakon kasar Sin na gudanar da wannan aiki tare ma da samar da kudin aiwatar da shi, ya nuna yadda ta damu da ayyukan kungiyar, kuma take fatan ganin nasarori da ci gabansu da ma hadin kansu wajen tunkarar kalubalen dake gabansu, bisa la’akari da yadda kasancewar sassan kungiyar a dunkule, zai rage kudin da ake kashewa tare da kara kaimi kan ayyukan da ake gudanarwa.

Kamar yadda jakadan na Sin a Nijeriya Cui Jianchun ya bayyana, ginin zai taka rawa wajen fadada dangantakar Sin da kasashen yammacin Afrika. A ganinsa, ba kyautata dangantakar Sin da kasashen zai yi ba kadai, har ma tsakanin kasashen kungiyar da kansu a wannan zamani da ake fuskantar dimbin klalubale. Baya ga haka, ya nuna yakinin da Sin ke da shi wajen ganin an samu hadin kai a tsakanin kasashen da ma karfin shawo kan matsalolin dake addabarsu.

Idan muka dubi mai masaukin baki wato Nijeriya da ta bayar da filin ginin, za mu gano cewa, ba kungiyar ECOWAS kadai ce za ta amfana da wannan alheri na kasar Sin ba, domin Nijeriya sai ta fi kowa cin moriya. Kamar yadda hedkwatar kungiyar tarayyar AU da Sin ta gina a Addis Ababa, ya kasance babba, kuma muhimmiyar alama, haka wannan gini ma zai zama wata babbar alama a bangaren gine-gine da kawata birnin Abuja. Haka zalika, tsawon lokacin aikin, zai bunkasa tattalin arzikin yankin da ma birnin, domin zai bude wata kasuwar hada-hada a kowanne bangare na kasuwanci. Har ila yau, zai samar da dimbin guraben ayyukan yi, wanda a ganina, za su rage zaman kashe wando tsakanin matasa da aikata miyagun ayyuka. Bugu da kari, fasahohin da Sin za ta yi amfani da su, zai kara ba Nijeriya gogewa da karin ilimi kan dabaru da fasahohin gine-gine na kasar Sin.

LABARAI MASU NASABA

Sin Na Goyon Bayan Najeriya Wajen Jagorantar Al’ummarta Zuwa Hawa Turbar Neman Ci Gaba Daidai Da Yanayin Kasar

Li Qiang Ya Zanta Da Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya

Kamar a ko da yaushe, kasar Sin ta cancanci yabo domin tana kara nuna matsayinta na babbar kasar da ta san ya kamata, kuma aminiya ta kwarai dake da burin ganin ci gaban kawayenta, kuma abun dogaro gare su. Hakika, al’ummar Nijeriya da ma Afrika, ba za su taba mantawa da alherin kasar Sin ba. (Fa’iza Mustapha)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sin Na Goyon Bayan Najeriya Wajen Jagorantar Al’ummarta Zuwa Hawa Turbar Neman Ci Gaba Daidai Da Yanayin Kasar
Daga Birnin Sin

Sin Na Goyon Bayan Najeriya Wajen Jagorantar Al’ummarta Zuwa Hawa Turbar Neman Ci Gaba Daidai Da Yanayin Kasar

November 4, 2025
Li Qiang Ya Zanta Da Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya
Daga Birnin Sin

Li Qiang Ya Zanta Da Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya

November 4, 2025
Tsohon Jami’in Diflomasiyyar Nijar: Baje Kolin CIIE Muhimmin Dandali Ne Na Bunkasa Hadin Gwiwa Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa
Daga Birnin Sin

Tsohon Jami’in Diflomasiyyar Nijar: Baje Kolin CIIE Muhimmin Dandali Ne Na Bunkasa Hadin Gwiwa Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa

November 4, 2025
Next Post
Nuna Bambanci Ga Sin Da Kayyade Hadin Gwiwa Tare Da Sin Ba Su Dace Da Moriyar Kowane Bangaren Duniya Ba

Nuna Bambanci Ga Sin Da Kayyade Hadin Gwiwa Tare Da Sin Ba Su Dace Da Moriyar Kowane Bangaren Duniya Ba

LABARAI MASU NASABA

tinubu

Tinubu Ya Umarci Ma’aikatar Ilimi Ta Kawo Ƙarshen Yajin Aikin ASUU

November 4, 2025
Sin Na Goyon Bayan Najeriya Wajen Jagorantar Al’ummarta Zuwa Hawa Turbar Neman Ci Gaba Daidai Da Yanayin Kasar

Sin Na Goyon Bayan Najeriya Wajen Jagorantar Al’ummarta Zuwa Hawa Turbar Neman Ci Gaba Daidai Da Yanayin Kasar

November 4, 2025
2027: Ko Kano Ta Zauna Lafiya Ko Ta Hautsine, Sai Mun Sauke Gwamna Abba — Shugaban APC

2027: Ko Kano Ta Zauna Lafiya Ko Ta Hautsine, Sai Mun Sauke Gwamna Abba — Shugaban APC

November 4, 2025
Li Qiang Ya Zanta Da Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya

Li Qiang Ya Zanta Da Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya

November 4, 2025
Karancin Abinci: Kofar Ofishin Tinubu A Rufe Take, Har Wasu Ministoci Ba Su Iya Ganinsa – Ndume 

Zargin Kisan Kiyashi Ga Kiristoci: Trump Bai San Ƙalubalen Tsaron Da Najeriya Ke Ciki Ba — Ndume

November 4, 2025
Tsohon Jami’in Diflomasiyyar Nijar: Baje Kolin CIIE Muhimmin Dandali Ne Na Bunkasa Hadin Gwiwa Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa

Tsohon Jami’in Diflomasiyyar Nijar: Baje Kolin CIIE Muhimmin Dandali Ne Na Bunkasa Hadin Gwiwa Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa

November 4, 2025
Zulum Ya Raba Motocin Sintiri 63 Ga Hukumomin Tsaro A Borno

Zulum Ya Raba Motocin Sintiri 63 Ga Hukumomin Tsaro A Borno

November 4, 2025
Shugaban Xi Ya Gana Da Firaministan Rasha

Shugaban Xi Ya Gana Da Firaministan Rasha

November 4, 2025
China Ta Gargaɗi Amurka Kan Tsoma Baki A Harkokin Nijeriya

China Ta Gargaɗi Amurka Kan Tsoma Baki A Harkokin Nijeriya

November 4, 2025
2023: Me Ya Sa Ake Rububin Wike?

Atiku Ya Fice Daga PDP Saboda Na Ƙi Bari Ya Lalata Mana Jam’iyya – Wike

November 4, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.