Da yammacin nan ne dai za a kara tsakanin Portugal da Switzerland a gasar cin kofin duniya da ke gudana a kasar Qatar.
Kocin tawagar kasar Portugal, Fernando Santos dai ya caccaki Cristiano Ronaldo a kan halin da ya nuna bayan da aka sauya shi daga wasan Portugal da Korea ta Kudu kuma bai bada tabbacin ko dan wasan zai buga wasansu da Switzerland ba a yau da dare.
Fuskar Ronaldo ta nuna ya fusata a lokacin da aka sauya shi daga wasan a minti na 65 a wasan da suka sha kashi da ci 2-1, inda na’urorin daukar hoto suka nuna fuskar dan wasan mai shekaru 37 cikin yanayi na gunaguni.
Bayan haka Ronaldo ya shiga musayar kalamai cikin fushi da wani dan wasan Korea, wato Cho Gue-Sung a yayin da yake barin filin wasa, kuma bayan wasan ne kocin ya gano yadda Ronaldo ya karbi sauya shi da aka yi.
Kocin ya kalli bidiyon, kuma bai ji dadin abin da Ronaldo ya yi ba, inda ya ce baya kusa da inda lamarin ya afku ba ballantana ya ji abinda ya ce, shi dai abin da ke gaban sa yanzu shine wasan su na yau.
Kawo yanzu dai an kammala wasa tsakanin kasar Morocco da Spain inda Morocco ta yi waje da Spain a bugun daga kai sai mai tsaron gida, inda Spain ta gaza jefa ko kwallo daya a ragar Morocco. Yayin da Morocco kuma kwallo daya kawai ta jefar a cikin guda hudu da ta buga.
Yanzu dai Kuma duk kasar data samu nasara tsakanin Portugal da Switzerland ita ce za ta kece raini da Morocco a wasan kwata fainal.