Wata girgizar kasa ta afku a babban tsibirin Java na kasar Indonesiya, akalla mutane 56 ne suka rasu inda daruruwan mutane kuma suka jikkata, kamar yadda hukumomin kasar suka bayyana.
Girgizar kasar mai karfin awo 5.6 ta afku ne a garin Cianjur da ke yammacin Java.
Hotunan bidiyo a shafukan sada zumunta sun nuna cewa anga wasu gine-gine sun koma kango da kayayyakin jama’a burjik a kan tituna.
Jami’ain sun yi gargadin cewa, adadin wadanda suka rasa rayukansu na iya karuwa.
Yankin da girgizar kasar ta afku yana da yawan jama’a kuma yankin na fama da zabtarewar kasa, sannan kuma yana da gine-gine marasa inganci.
Gwamnan jihar Java ta Yamma Ridwan Kamil ya tabbatarwa kafafen yada labaran kasar cewa mutane 56 ne suka rasu sannan sama da 700 sun jikkata.