Yanayin girgizar-kasa mai karfin gaske da ta auku a kasashen Turkiyya da Siriya ya jefa duniya cikin alhini sakamakon dubban mutanen da suka rasa rayukansu da kuma wadanda suka jikkata, ya zuwa ranar laraba an tabbatar da mutuwar mutum 7,000.
Rabon a ga girgizar-kasa mai barna irin wannan a duniya tun a shekarar 1999 lokacin da kimanin mutum dubu 17 suka rasa rayukansu.
Bayan aukuwar lamarin dai, masu aikin ceto sun dukufa fafutikar ganin ko za a samo wasu da ransu a karkashin baraguzan gine-ginen da suka rufta a wasu yankunan kasashen Turkiyya da Siriya.
Sai dai ruwan sama mai karfi da dusar kankara wadda ke zuba sun rika kawo cikas ga aikin a kudu maso gabashin Turkiyya.
Shafin Hausa na BBC ya ruwaito Hukumar Lafiya ta Duniya na gargadin cewa akwai yiwuwar yawan wadanda suka rasa ransu a lamarin zai yi matukar karuwa.
Mutane da dama a yankunan da lamarin ya faru na jin tsoron komawa cikin gine-gine da suka rage.
Masu nazari kan motsin kasa sun ce girgizar ita ce mafi girma da aka taba samu a Turkiyya.
Al’ummar yankin sun ce an kwashe minti biyu kasa na jijjiga kafin lamarin ya dakata.
Alkaluma daga Turkiyya da Siriya na nuna cewa kawo yanzu mutum fiye da dubu biyar ne suka mutu sannan fiye da dubu 15 suka jikkata sakamakon ibtila’in girgizar kasar.
Shugabanni kasashen duniya sun yi alkawarin aikewa da tawagar ma’aikata da kayan aikin ceto ya zuwa Turkiyya don agazawa.
Rahotanni na cewa an kara samun girgizar kasa karo na biyu cikin kwana guda a kudu-maso-gabashin Turkiyya.
Hukumar lura da yanayin kasa ta Amurka ta ce karfin girgizar kasar ya kai 7.5 a kan ma’auni.
Lamarin ya faru ne a gundumar Elbistan na lardin Kahramanmaras.
Wani jami’in Hukumar Lura da Bala’o’i na Turkiyya ya tabbatar da cewa “wannan wata sabuwar girgizar kasa ce ba ragowar wadda ta faru ne a farko ba.”
Wani faifan bidiyo ya nuna yadda mutane ke gudu cikin rudewa a lokacin da girgizar ta biyu ta faru.
An ga mutanen suna ihu, suna gudu a kan tituna a lokacin da kura ke lafawa bayan gine-gine sun rufta.
Girgizar kasar mai karfin maki 7.8 ta afka wa yankin Gaziantep da ke kudancin Turkiyya a tsakiyar daren Litinin.
Kuma an jiyo ruguginta har a yankin Gaza. An kuma samu rushewar gidaje a Lebanon.
Turkiyya dai ta ayyana dokar ta baci tare da kira ga mutane su dakatar da amfani da wayoyinsu, saboda masu aikin agaji su samu damar kai wa ga wadanda suka makale a cikin baraguzai.