Yau ne, ma’aikatar masana’antu da fasahar sadarwar zamani ta kasar Sin, ta shirya taron manema labarai, don gabatar da ayyukan gwamnati game da ingantawa da daga matsayin masana’antun samar da kayayyakin masarufi a cikin shekaru 10 da suka gabata.
Wakilin CMG ya bayyana cewa, a cikin shekaru 10 da suka gabata, an samu ingantuwar hazaka a fannin masana’antun samar da kayayyakin masarufi na kasar Sin, haka kuma an kara habaka ma’auni da cikakken karfin masana’antun yadda ya kamata.
A cikin shekaru 10 da suka gabata, yawan manyan kamfanoni a bangaren masana’antun samar da kayayyakin masarufi na kasar Sin, ya karu da kashi 23.7 cikin 100 zuwa 172,000, kana karin darajar masana’antun ya kai kashi 27.9 cikin 100 kan masana’antun kasar, yayin da kudaden shiga na aiki da ribar da masana’antun ke samu, sun karu da kashi 35 bisa 100 da 64.5 cikin 100 bi da bi a cikin shekaru 10 da suka gabata. (Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa)