Har yanzu dai muna kan bayani game da garin da Allah ya rantse da shi kuma aka halatta wa Annabi (SAW) shi kadai kuma aka haramta wa kowa. Abin da ake nufi da wannan gari (a cikin surar ta Balad) da aka yi rantsuwa da shi wurin wadannan Malaman Tafsiri shi ne garin Makka.
Amma shi Malam Wasidi ya ce ai ma’anar abin tana nufin ya Manzon Allah, Allah yana rantsuwa gare ka ne da wannan gari wanda ka daukaka shi saboda zaman da ka yi a ciki kana raye, garin kuma ya samu albarkarka bayan Allah ya tafi da kai wurinsa (wafati). Wannan garin a wurin Malam Wasidi Madina ake nufi. Allah yana rantsuwa da Madina saboda Manzon Allah ya zo ya daukaka ta yana raye kuma ya girmama ta da albarkarsa bayan komawarsa wurin Allah. Shi ya sa kowane masoyi yake begen ya je Madina ya ziyarci Manzon Allah (SAW).
- Harin Tudun Biri: Gwamnatin Kaduna Da ANRiN Sun Raba Kayan Abinci Da Irin Noma Ga Magidanta 100
- Tinubu Ya Tafi Kasar Qatar Don Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Kasuwanci
Sai dai, fassarar farko da take cewa Makka ake nufi ta fi inganci domin surar (Balad) a Makka ta sauka. Kuma maganar da ta biyo bayan ayar tana kara inganta wannan saboda fadin Allah Ta’ala, “an halatta ma wannan gari”. To idan aka bi ta haka, ita ma Madina; Manzon Allah (SAW) ya haramta ta, kamar yadda Allah ya haramta Makka, Manzon Allah ya ce shi ma ya haramta Madina har ma ya ce “duk wanda aka gan shi yana saran bishiyar Madina ko faruta a ciki, na ba wa wanda ya gan shi kyautar kayan da ke jikin mutumin (mai farauta ko sare bishiyar)”.
Akwai Sahabin da ya ga wani yana farauta a Madina ya kama shi da karfin tsiya ya cire kayansa, aka kai shi kotu, ya ce Manzon Allah (SAW) ne ya ce ya bayar. Aka ce ya kawo shaida a kan haka kuma ya kawo wadanda suka ji daga Manzon Allah (SAW). Shi ya sa yadda ake yin awon duk abin da mutum zai taba (na biyan fansa) a Makka ita ma Madina sai an yi mata. Iyakar haramin Madina kamar yadda Manzon Allah ya ce “tun daga Dutsen Iru har zuwa Dutsen Sauru”. Dutsen Sauru yana nan bayan Dutsen Ukhudu.
Shi kuwa, Ibin Ada’in shi ya tafi ne a kan garin nan Makka ne. Ya ce Allah ya amintar da Makka saboda zaman Manzon Allah a ciki. Domin duk inda Manzon Allah yake amana ne ga wannan wajen.
Ita dama amanar da Allah ya ba mu guda biyu ce, suna nan a cikin Alkur’ani. Amana ta farko Allah ba zai yi wa al’ummar Annabi (SAW) azaba ba idan yana cikinsu kamar yadda ya fada a cikin Suratu Lanfali: “Allah ba zai yi wa al’ummarka azaba ba alhali kana cikinsu”. In dai Manzon Allah yana cikin al’umma to amana tana cikinsu. Kafirai suna ta cewa azabar da ake fada ta zo mana, amma Allah ya ce ba zai kawo ta ba sai Manzon Allah ya tafi. To kuma da yake Manzon Allah (SAW) mai tausayi ne sai ya yi kankan da kai a wurin Allah ya ce “Allah idan ka tafi da ni ya za ta kasance kenan (dangane da azabar)?” Sai Allah ya saukar ma sa da “Allah ba zai yi musu (al’ummarka) azaba ba in dai suna Istigfari”. Manzon Allah (SAW) Allah ya zo da amana biyu, in dai yana nan a doron kasa shi amana ne ga al’umma azaba ba za ta sauka ba, in kuma ba ya nan ga Istigfari nan mu rike mu nemi gafarar zunubanmu; shi ma amana ne.
To cewa duk inda Manzon Allah yake, amana tana nan a wurin, shi ya sa ake tawassuli da shi; da sifofinsa wurin rigakafin bala’o’i.
Allah ya yi rantsuwa da Makka ne saboda Manzon Allah yana ciki (a wata fassarar) ko kuma Allah ba zai yi rantsuwa da Makka ba idan Manzon Allah ba ya ciki (a fassarar harafin korewa kenan na farkon surar). Shi ya sa a wurin Imam Malik da Imam Shafi’i Madina ta fi Makka.
Wata alama kuma da ke kara nuna girmamawar da Allah ya yi wa Manzon Allah (SAW) a cikin surar ita ce; Allah ya yi rantsuwa da uba da dan da uba ya haifa: “wa walidun wa ma walada”. Wasu da suka tafi a fassara ta gamewa suka ce Allah yana nufin ya rantse da Annabi Adamu (AS) da abin da ya haifa, shi ne zuriyyarsa baki daya. Aka ce Allah ya yi rantsuwa da Annabi Adamu (AS) da zuriyyarsa ne saboda su ne cikakkun halitta duk gaba daya. Duk cikin halittar Allah babu kamar Dan Adam, hatta Mala’iku Dan Adam suke wa aiki, akwai mai shirya wa Dan Adam arziki kamar Mika’ilu, da mai kawo masa ruwa, da mai busa masa rai, da mai kashe shi, da wanda ake aiko shi wurin Dan Adam (Jibrilu), da masu bude wa Dan Adam aljanna (Allah ya sa muna ciki) da masu bude masa wuta (a’uzu billahi), kun ga duk hidimar Dan Adam suke yi bisa umurnin Allah. Don haka aka ce Allah ya yi rantsuwa da Annabi Adamu uban mutane da kuma ‘ya’yansa. Saboda girman Dan Adam, Allah ya kira shi da Khalifansa wanda babu wata halitta da Allah ya kira ta da hakan. Idan an ji ana sa khalifanci to babu asalin maigida ne, amma Allah da yake madayanci tabbatacce yana nan amma saboda girmamawa sai ya nada Dan Adam Khalifansa domin duk abin da za a karba a wurinsa na ibada da sauran su wurin Dan Adam za a zo a karba. Idan mara lafiya ne kar ya ce shi wurin Allah zai karbi magani, a’a, tafi asibiti wurin likita shi ne Khalifan Allah a can. Wurin ilimi a tafi wurin Malami shi ne Khalifa ta nan. To, duk wanda ya ce ayar tana nufin Annabi Adamu da ‘ya’yansa bani Adam, ya yi fassara ce mai gamewa.
Wasu malamai kuma sun ce uban da aka rantse da shi shi ne Annabi Ibrahim (AS), wato shi ne uban garin Makka, shi ya gina Ka’aba, shi ya kawo dansa Isma’il da matansa Hajara garin, a lokacin da ya kawo su wurin fako ne babu kowa. Bisa hakan sai wasu malamai suka ce ana nufin da uban garin (Makka) Annabi Ibrahim kenan da kuma dan da za a haifa a garin Annabi Muhammadu (SAW).
Annabi Ibrahim ya yi addu’a dama cewa Allah ya aiko da babban Manzo daga cikin ‘ya’yansa. Sannan Annabi (SAW) yana cewa “ni addu’ar babana Ibrahim ce”.
Sai Malamai suka ce to duk wanda ya yi fassarar cewa uban ana nufin Annabi Ibrahim, dan kuma ana nufin Annabi Muhammadu haka abin yake insha Allah. Domin wannan nuni ne izuwa ga Manzon Allah (SAW), idan ka duba surar za ka ga ta tattara rantsuwa da Annabi (SAW) daga ayar farko zuwa wannan.
Malamai sun ce Allah ya kiyaye mu al’ummar Manzon Allah, don da akwai inda al’ummar za ta bata to da a nan ne. Saboda irin wannan ne ya sauka ga nasara “wa walidun wa ma walada”, sai suka ce uba ana nufin Allah da wanda ya haifa shi ne Annabi Isah (AS). Amma mu al’ummar Annabi Muhammad (SAW) Allah ya kiyaye mu, babu wanda ya taba cewa “wa walidun” ana nufin “Allah uba”, a uzu billahi.