Gwamnatin Jihar Kaduna da hadin ma’aikatar lafiya, wanda bankin duniya da kungiyar kula da lafiyar iyali ke tallafawa a Nijeriya (ANRiN) sun raba kayan abinci da kayan amfanin gona ga magidanta 100 da harin Tudun Biri na Sojoji ya rutsa da su.
In ba a manta ba, al’ummar Tudun Biri, da ke karkashin karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna, sun fuskanci wani mummunan hari da jirgin yaki mara matuki na Sojoji a ranar 3 ga watan Disamba, wanda yayi sanadin mutuwar mutane da dama tare da jikkata wasu.
- Gwamnatin Tarayya Za Ta Zartar Da Dokar Karya Farashin Magunguna
- Mazauna Yankunan Karkarar Sin Sun Samu Karin Kyautatuwar Rayuwa
Tallafin ga al’ummar Tudun Biri, wani shiri ne na gwamnatin jihar a karkashin ma’aikatar lafiya, wanda bankin duniya da kungiyar kula da lafiyar iyali ke tallafawa, wanda ANRiN ke aiwatarwa.
ANRiN wani shiri ne na Babban Bankin Duniya ke tallafawa da abinci mai inganci da gina jiki ga mata masu juna biyu da masu shayarwa, ‘yan mata matasa, da yara ‘yan ƙasa da shekaru 5.
Shirin wanda ya kunshi jihohi 12 na Nijeriya da ke fama da matsalar karancin abinci mai gina jiki, wanda Kaduna ke daya daga cikinsu.