A wani labarin na daban kuma, Masu rajin kare hakkin bil’adama na jimamin rasuwar wani jagorar yawon bude ido dan kasar Zimbabwe da wata giwa ta tattake har ya mutu a wani gandun daji na Gondwana da ke Afirka ta Kudu.
Dabid Kandela, mai shekaru 36, yana jagorantar gungun masu yawon bude ido ne a yammacin Lahadin da ta gabata, lokacin da bala’in ya faru, in ji masu kula da gandun dajin a cikin wata sanarwa da kafofin yada labarai na kasar suka ruwaito.
- Kafa Jam’iyyar Adawa: Atiku Da Wasu Sanatoci Sun Sake Sabon Yunkuri
- Kabilu Biyar Mafiya Tsadar Aure A Nijeriya
Ya kara da cewa lamarin ya faru ne yayin da tawagar giwaye ke wucewa ta sansanin Eco na Gondwana.
Sanarwar ta kara da cewa, “Tawagar giwayen sun kusa wucewa ta sansanin lokacin da Kandela ya ci karo da giwa ta karshe da ta rage kafin afkuwar lamarin.”
Abokan jagororin yawon bude ido da masu gudanar da yawon shakkatawa sun bayyana Kandela a matsayin kwararre mai jagora wanda ke da sha’awar aikinsa.
Sun ce ba kasafai irin wannan lamarin ke faruwa ba.
Giwaye dai sun kasance babban abin sha’awar gani a lokacin yawon bude ido a Kudancin Afirka.