Mutane biyar ne suka mutu sakamakon wata gobara da ta tashi a wani wurin ajiye haramtaccen tataccen man fetur a Omoku da ke karamar hukumar Ogba/Egbema/Ndoni a jihar Ribas.
Kungiyar Matasa da kula da Muhalli ta yankin Neja Delta, (YEAC-Nigeria), a wata sanarwa da ta fitar a Fatakwal da safiyar Lahadi, ta ce lamarin ya faru ne da safiyar ranar Asabar.
Sanarwar mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar YEAC-Nigeria, Dr. Fyneface Dumnamene Fyneface, ta ce wadanda lamarin ya rutsa da su, akwai mata hudu da namiji daya, wadanda sun kone, irin yadda ba a iya gane su.