Gobara ta kone rumbun ajiyar kayayyaki na cibiyar bayar da agaji da kawar da talauci ta Kasa (NSIPA) da ke Unguwar Idu a Abuja, inda ta kone kayayyakin horo na biliyoyin Naira.
Karamin minista a ma’aikatar jin kai da rage radadin talauci, Dakta Yusuf Sununu, ya tabbatar da faruwar lamarin yayin da ya kai ziyarar gani da ido a rumbun ajiyar, inda ya tabbatar da cewa za a dauki matakan da suka dace don hana afkuwar irin wannan lamarin a nan gaba.
- Gwamnoni Sun Miƙa Ta’aziyya Ga Waɗanda Wani Abu Ya Fashe Da Su A Mota A Zamfara
- Ban Ce Ina Goyon Bayan Dokar Haraji Dari Bisa Dari Ba – Kofa
Sununu ya kuma bayar da umarnin kafa kwamitin mutum biyar da zai binciki lamarin gobarar, inda ya kara da cewa an ware kayan aikin ne domin horar da masu cin gajiyar shirin N-Power a karkashin NSIPA.
A cikin wata sanarwa da daraktan yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar, Rhoda Ishaku, ya bayyana cewa kwamitin na da mako biyu domin gabatar da rahotonsa.
Sununu ya yaba da kokarin hukumar kashe gobara ta tarayya (FFS), hukumar kashe gobara ta babban birnin tarayya (FCT), da ‘Julius Berger’ bisa kokarin da suka yi na kashe gobarar.
Ya kuma yaba wa rundunar ‘yansanda reshen ‘Life Camp’ da suka tsare rumbun don tarwatsa masu yunkurin sace abin da ya rage bai kone ba a rumbun.