Al’ummar unguwar Madina Kwatas sun tashi da mummunar ibtila’in gobara wacce ta yi sanadin rasa yara kanana biyu – Zainab Bashir Muhammad (Hibba) mai shekara 7 da kuma Ummu Salma Bashir (Afnan) mai shekara 5 a duniya.
Gobarar wacce ta tashi a makwabtar wakilinmu da ke unguwar Madina quarters a kusa da makarantar Barden Gabas da ke yankin Turwun, ya rahoto cewa, gobarar ta tashi ne da misalin karfe 11 na safiyar ranar Lahadi.
- Rukunin Farko Na Masu Yawon Bude Ido Da Suka Samu Bizar Tashar Shige Da Fice Ya Isa Xinjiang
- Dokar Masana’antar Fetur (PIB): Yadda Aka Yi Wa Kudin Man Fetur Kofar-raggo A Nijeriya
Abun da ya faru kuwa shi ne, mahaifiyar yaran ta fita unguwa inda ta bar yaranta biyu a cikin daki bayan ta kulle dakin tare da kofar gida.
“Lokacin da muka ji wutar ta tashi mun nufi gidan ni da makwabtana, mun yi duk kokarin balle kofar gidan amma hakan ya cutura sai da aka nemo guduma aka balle. Ana wannan gabar, mun yi kokarin haurawa gidan ta sama, inda muka tarar da wutar ci karfin dakin da yaran suke.
“Bayan shiganmu cikin gidan, mun yi kokarin balle kofar dakin amma hakan ba ta yiwu ba. Wuta ce sosai da hayaki mai illa matuka,” In ji wakilinmu da lamarin ya wakana a kan idonsa.
Kazalika, Usman Abdullahi (Dan Usmanu) ya shaida cewar, “Allah dai ya aiko da tsautsayi amma ba dabi’ar matar ba ne kulle yara a gida. Wani lokacin in za ta fita ta na kawo yaranta gidana saboda gidan na kusa da kofar gidana.
“Mijinta mai suna Bash baya nan a lokacin da wutar ta tashi. Har yanzu dai ba mu gano hakikanin abun da ya janyo tashin wutar ba.
“Sai dai abun takaici duk da kokarin namu mun kasa ceto yaran. Allah sa masu ceto ne.”
“Babu abun da aka cire a cikin gidan komai ya kone kurmus. Dabbobi ne kawai mutane suka iya cirosu ta saman garu, amma bayan tumakin gidan komai ya kone kurmus.”
Wakilinmu ya kuma shaida mana cewar, jami’an kashe gobara na jihar sun yi kokarin zuwa a kan lokaci wanda sun bada gagarumin gudunmawa wajen kashe wutar.
Sai dai lamarin ya tayar wa al’ummar unguwar hankali matuka.
Tuni aka yi jana’izar yaran kamar yadda addinin musulunci ya tanadar.