Wata gobara da ta tashi a daren jiya Litinin a garin Ilorin babban birnin jihar Kwara ta kone Shaguna 15 kurmus da lalata kayan da aka kiyasata kundin su ya kai naira miliyan 19.5.
Iftila’in ya afku ne a wani katafaren ginin Atiba- Iyalamu da ke dauke da shagunan a daura da yankin Oja- Tuntun.
An kiyasta cewa, sauran kayan da suka rage gobarar bata kone ba a shaguna biyar, sun kai na naira miliyan 10.7.
Mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar Kwara Hassan Adekunle, ya tabbatar da afkuwar lamarin, inda ya ce Shagunan 15 ne suka kone a ginin wanda ke dauke da shaguna 20.
A cewar Adekunle, “Gobarar ta tashi ne a daren jiya litinin wacce kuma ba ayi saurin fahintar tashin gobarar ba har sai da tayi karfi kafin jami’an hukumar kashe gobara ta jihar suka kawo dauki wurin kashe ta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp