Wata gobara ta sake tashi a fitacciyar Kasuwar Kara da ke Sokoto, wacce aka fi sani da sayar da hatsi da kayan abinci, inda ta cinye gaba ɗaya kasuwar tare da mayar da shaguna da wuraren ajiyar kaya toka.
Gobarar ta fara ci ne da safiyar Asabar, inda jami’an kwana-kwana suka yi ƙoƙarin shawo kanta amma ta gagara. Har yanzu ba a gano musabbabin tashin gobarar ba.
- Turji Ya Ƙaƙaba Wa Ƙauyen Mataimakin Gwamnan Sokoto Da Wasu Biyan Harajin Miliyan 22
- Gwamnatin Sokoto Za Ta Kashe Naira Miliyan 998 A Cibiyoyin Ciyarwa Na Ramadan
A halin yanzu, masu shaguna da gidaje da ke kusa da kasuwar na kwashe kayansu saboda tsoron sake ɓarkewar wutar. Hukumar kasuwar ba ta samu damar yin jawabi ba domin suna ƙoƙarin hana mutane yin amfani da iftila’in don yin sata.
A baya-bayan nan, wani ɓangaren kasuwar da ake amfani da shi wajen niƙa ya kone ƙurmus, inda gwamnatin jihar ta alkawarta tallafa wa waɗanda gobarar ta shafa.














