Wata gobara ta sake tashi ta ƙone wani ɓangare na fitacciyar Kasuwar Oba da ke tsakiyar Birnin Benin, a Jihar Edo, a daren ranar Laraba.
An ruwaito cewa kayayyaki da darajarsu ta kai miliyoyin Naira sun ƙone sakamakon gobarar.
- Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0
- Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya
Masu shaguna da suka isa kasuwar lokacin da wutar ke ci sun kasa yin komai sai kallo yayin da ma’aikatan kashe gobara ke ƙoƙarin kashe wutar.
A lokacin da haɗa wannan rahoto, ba a gano musabbabin tashin gobarar ba.
Gobara ta taɓa ƙone kasuwar a zamanin tsohon gwamnan jihar, Godwin Obaseki, kuma yanzu haka ana sake gina ta ƙarƙashin gwamnatin Gwamna Monday Okpebholo.
Shugaban ƙaramar hukumar Oredo, Hon. Gabriel Iduseri, ya ziyarci kasuwar da safiyar ranar Alhamis.
Yayin ziyararsa, Iduseri, ya bayyana lamarin a matsayin babban iftila’i ga ‘yan kasuwa, tare da alƙawarin cewa za su ba su tallafi.
“Wannan lokaci ne na matuƙar baƙin ciki ga mutanenmu, musamman ma ‘yan kasuwar da suka dogara da wannan waje don samun abincin yau da kullum. Ba za mu bar su su fuskanci wannan asara su kaɗai ba,” in ji shi.