Gobara ta tashi a fitacciyar Kasuwar Alaba da ke Legas da yammacin ranar Talata, inda shaguna da kayan miliyoyin Naira suka ƙone ƙurmus.
Wani mai suna KB Clothings ne, ya wallafa bidiyon tashin gobarar kai-tsaye a Tiktok, inda ya nuna yadda gobarar ke bazuwa cikin kasuwar, yayin da ‘yan kasuwa ke kuka suna neman agaji.
- Gwamnoni Sun Yi Ta’aziyyar Mutanen Da Suka Rasu A Fashewar Tankar Mai A Neja
- Aikin Jinya Kyauta: Gwamnatin Zamfara Ta Kammala Zagaye Na 10 Na Kula Da Marasa Lafiya 3,447
Wasu kuma sun yi ƙoƙarin fito da kayansu kafin wutar ta ƙara bazuwa.
Jami’an Hukumar Kashe Gobara da Ceto na Jihar Legas, sun isa kasuwar, inda suka yi ƙoƙarin kashe wutar.
A halin yanzu, babu wata sanarwa a hukumance daga hukumar kashe gobara ta jihar.
Cikakken bayani na tafe…