Gobara ta babbake kasuwar ‘yan Katako da ke Muda Lawan a cikin kwaryar Bauchi, lamarin da ya tada hankalin al’umma da dama.
Wakilinmu da ya ziyarci wajen ya ga dandazon jama’a na ta kokarin kashe gobarar amma sakamakon cewa wutar ta kama sosai ta ki mutuwa.
- Ba A Son Raina Ummita Ta Rasu Ba –Dan China
- Ministan Kudin Habasha Ya Yaba Da Kokarin Sin Kan Ci Gaban Kasa Mai Inganci
Lamarin dai ya auku ne da misalin karfe 7 na daren yau.
Ya zuwa yanzu jami’an Hukumar Kashe Gobara na jihar, na kokarin gane sun kashe wutar.
Wutar na cigaba da ci sosai kuma ba a san adadin shagunan da suka kone kawo yanzu ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp