Wata mummunar gobara da ta tashi a wata makarantar Islamiya da ke ƙaramar hukumar Kaura-Namoda, ta Jihar Zamfara ta hallaka aƙalla ɗalibai 17, tare da jikkata wasu 16.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa gobarar, wadda ta fara ci a daren a ranar Talata, ta ɗauki sama da sa’o’i uku kafin a samu damar shawo kanta, wanda duk da haka ta haddasa babbar asara da kuma rashi mai ban tausayi.
- Yaƙi Da Ta’addanci: Gwamna Lawal ya Yaba Wa DSS Kan Bankaɗo Makamai A Jihar Zamfara
- Sojoji Sun Ƙwato Makamai, Sun Ci Gaba Da Neman Bello Turji A Zamfara
Wasu mazauna yankin sun ce gobarar ta fara ne daga wani wuri da ake ajiye katako, wanda ake kira “kara” a yankin, sannan ta bazu har cikin ɗakin karatun Makarantar Mallam Ghali, inda sama da ɗalibai 100 ke taruwa.
Sun ƙara da cewa bayan an ceto daliban, an yi tunanin babu kowa a ciki, amma daga bisani da suka dawo bayan an kashe gobarar, sai suka fara ganin hannaye da kafafu na mutanen da suka kone kurmus ta yadda ba a iya gane su.
Da yake magana ta wayar tarho game da mummunar gobarar, Shugaban ƙaramar hukumar Kaura-Namoda, Comrade Mannir Muazu Haidara, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce yana kan hanyarsa domin duba halin da ake ciki kuma zai bayar da karin bayani daga baya.