Watanni takwas bayan dakatar da zirga-zirgar jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna, biyo bayan harin ‘yan ta’adda a ranar 28 ga watan Maris na wannan shekara, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 11 tare da jikkata wasu da dama, gwamnatin tarayya ta hannun ma’aikatar sufuri ta tarayya ta sanar da cewa za ta dawo da zirga-zirgar jirgin a gobe Litinin. Gwamnatin ta gindaya sabbin sharudda ga fasinjoji.
A cewar wata sanarwa da mahukuntan kamfanin suka fitar kuma aka baiwa LEADERSHIP, sun ce kowanne fasinja sai ya nuna takardar katin shaidan dankasa kafin a sayar masa da tikitin shiga jirgin.
Hukumar ta kuma bayyana dalla-dalla cewa fasinjojin dake da sahihin tikiti ne za a basu damar shiga dakunan tashi da sauka na tashoshin jirgin kasan da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Jirgin fasinja zai fara da jigilar fasinjoji daga Tashar Idu (Abuja) da karfe 9:45 na safe, Kubwa (Abuja) zuwa Rigassa (Kaduna) 10:06 na safe; sai kuma na yamma daga tashar Idu (Abuja) 3:30 na rana, Kubwa (Abuja) da karfe 3:50 na yamma.