Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai tafi kasar Guinea-Bissau a ranar Asabar don halartar taro karo na 63 na Hukumar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afrika (ECOWAS).
A wata sanarwar da kakakin shugaban kasan, Dele Alake, ya ce taron ana tsammanin za a gudanar da shi ne a ranar Lahadi, kuma za a tattauna muhimman batutuwan da suka shafi matsalar tsaro, sha’anin kudi, kasuwanci, tare da tattaunawa kan rahoton yanayin sauyin gwamnati a Jamhuriyar Mali, Burkina Faso da kuma Guinea.
- An Bude Taron Duniya Kan Fasahar Kwaikwayon Tunanin Dan Adam Ta AI A Shanghai
- Hare Haren Bindiga Sun Rushe Bikin Murnar Ranar Samun ‘Yancin Kan Amurka
Shugaban zai tafi da masu ba shi shawara da wasu jami’an gwamnatin Nijeriya.
Kuma zai dawo Nijeriya da zarar aka kammala taron.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp