Fitaccen dan jaridan nan kuma mawallafi, Peter Enahoro, da aka fi sani da Peter Pan, ya kwanta dama.
Enahoro ya rasu ne a kasar Birtaniya bayan fama da wata cutar da ba a bayyanata ba, ya kuma bar duniya ne yana da shekara 88 a duniya.
- APC Ta Kori Dan Takarar Gwamna Da Zababben Sanata A Jihar Taraba
- An Samu Gobara 258 Cikin Wata 3 A Jihar Kano
Wata fitacciyar ‘yar jarida a Nijeriya, Misis Bunmi Sofola, ce ta sanar da mutuwar marubucin a wata sanarwar da ta fitar cikin jimami a ranar Litinin, ta ce, Ehanoro ya mutu ne a ranar Litinin 24 ga watan Afrilu na shekarar 2023.
“Ina bakin cikin sanar da rasuwar kwararren madubin dan jaridanmu, Peter Enahoro da aka fi sani da ‘Peter Pan’ a kasar Landan yana da shekara 88 a duniya.”
“An misalta Enahoro a matsayin wanda ake tunanin shi ne dan jarida a Afrika da ya fi shahara a duniya,” Sofola ta shaida.
Ehanoro yana cikin tsoffin ‘yan jarida a Nijeriya kuma ya zama Editan jaridan Daily Times tun yana karamin shekaru.
Marigayin ya halarci Kwalejin Gwamnati a Ughelli da yanzu take jihar Delta, kuma ya zauna tare da fitaccen Farfesan Ingilishi na farko a Afrika, JP Clark.
Ya kasance Editan da ke bada gudunmawa a gidan rediyon Deutsche Welle a Cologne da ke Jamani a tsakanin 1966 zuwa 1976, Kuma Editan Afrika na National Zeitung, a Basel ta kasar Switzerland, kuma ha zama daraktan editoci na mujallar New African magazine a London a shekarar 1978.