Goman ƙarshen Ramadan su ne mafi girman dararen duniya baki ɗaya, domin a cikinsu Lailatul-Ƙadari yake. Allah Ta’ala Yana cewa: “Lailatul-Ƙadari ya fi wata dubu alheri” Suratul Ƙadri aya ta 3.
Babban malamin tafsiri al-Imam al-Bagawi, Allah Ya yi masa rahama yana cewa: “Malaman tafsiri sun bayyana ma’anar ayar da cewa: aikata aikin ƙwarai a cikin daren Lailatul-Ƙadari shi ne ya fi alheri sama da aikin ƙwarai a cikin watanni dubu wanda babu Lailatul-Ƙadari a cikinsu”
Hadisi ya tabbata a cikin Al-mujtaba na Imam an-Nasa’i da Musnad na Imam Ahmad daga Abu Huraira Allah Ya ƙara yarda a gare shi ya ce: Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Ramadana ya zo muku, wata ne mai wata irin albrka, Allah Mai girma da ɗaukaka ya wajabta muku azumtar sa, ana buɗe ƙofofin Aljanna a cikinsa, ana kuma rufe ƙofofin Jahannama a cikinsa, a cikinsa akwai wani dare da ya fi wata dubu alheri, duk wanda aka haramta masa alherinsa, to, tabbas an haramta masa alheri”
Ya zo a cikin Sahihul Bukhari da Muslim, Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Duk wanda ya tsayu a daren Lailatul-Ƙadari yana mai imani da neman lada, to, an gafarta masa zunubansa”
Wannan dare yana cikin goman ƙarshe na Ramadan. Manzon Allah (S.A.W) ya kasance yana cewa da Sahabbai: Ku kirdadi Lailatul-Ƙadari a goman ƙarshe na Ramadan. Bukhari da Muslim ne suka ruwaito.
Ana karɓo hadisi daga Nana Aishatu, Allah Ya ƙara yarda a gare ta, ta ce: Lalle Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Ku kirdadi Lailatul-Ƙadari a cikin dare mara na goman ƙarshe na Ramadana” Bukhari da Muslim ne suka ruwaito.
Manzon Allah (S.AW) ya fi kowa girman matsayi da alfarma da daraja da martaba a wurin Allah. Allah Ya gafarta masa abin da ya aikata da wanda bai aikata ba amma duk da haka yana ƙara ƙaimi da ƙwazo a goman ƙarshe na Ramadan sama da ƙwazonsa a goman farko da ta tsakiya na wannan wata mai albarka. Nana Aisha Allah Ya ƙara mata yarda ta ce: “Manzon Allah (S.A.W) ya kasance idan goman ƙarshe ta shiga, sai ya ƙara zage dantse, ya kuma raya daren gaba ɗaya, kuma ya tayar da iyalansa daga barci” Bukhari da Muslim ne suka ruwaito. A wata ruwaya ta Muslim cewa ta yi:” Manzon Allah (S.A.W) ya kasance yana ƙoƙari a goman ƙarshe irin ƙoƙarin da baya yinsa a waninsa”
Sayyadina Aliyu ɗan Abu Ɗalib, Allah Ya ƙara masa yarda ya ce: “Lalle annabi (S.A.W) ya kasance yana tayar da iyalansa a goman ƙarshe na Ramadana” Tirmizi ne ya ruwaito da salsala ingantacciya.