Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya rattaba hannu kan kudirin dokar kare masu bukata ta musamman ta Jihar Gombe ta 2024, wadda ta share fagen kafa hukumar masu bukata ta musamman a jihar.
Dokar mai matukar muhimmanci za ta kafa tsarin tallafawa da damawa da masu bukata ta musamman, da tabbatar da adalci a zamantakewa da kare hakkin masu bukata ta musamman (PWDs) a jihar.
- Gaza: Ana Gudanar Da Kirismeti Lami A Bethlehem Mahaifar Yesu Almasihu
- Manyan Bankunan Kasa Na Sin Da Nijeriya Sun Sabunta Yarjejeniyar Musayar Kudi
Yayin bikin rattaba hannu kan kudirin dokar wanda ya gudana a gidan gwamnati, Gwamna Yahaya ya nada shugaban kungiyar masu bukata ta musamman ta kasa reshen Jihar Gombe, Dakta Ishiyaku Adamu, a matsayin babban sakataren hukumar ta masu bukata ta musamman.
Gwamnan ya yi amfani da wannan damar wajen sanar da masu bukata ta musamman kan umarnin da ya bayar na gyara da sake fasalin makarantar masu bukata ta musamman daya tilo da ke jihar.
Ya yaba wa ‘yan majalisan dokokin Jihar Gombe bisa jajircewar da suka yi wajen zartar da kudirin, ya kuma yaba da gudunmawar kungiyoyin fafutuka da masu ruwa da tsaki wadanda suka jajirce wajen ganin an kafa wannan doka.
Da yake jawabi a wajen taron, Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Gombe, Rt. Hon. Abubakar Mohammed Luggerewo, ya bayyana cewa majalisar ta yi nazari sosai kan kowane bangare na kudirin don tabbatar da amincewar ta yi daidai da muradun masu bukata ta musamman.