Hukumar Kula da Ci gaban Fasahar Sadarwa ta Kasa (NITDA), ta bayyana cewa kamfanonin Google, Microsoft, da TikTok sun biya harajin Naira tiriliyan 2.55 ga gwamnatin Nijeriya a farkon rabin shekarar 2024.
Hakan na cikin wata sanarwa da Hadiza Umar, Daraktar Sadarwa da Hulɗa da Jama’a ta NITDA, ta fitar, bayan tattara bayanai daga Hukumar Tara Haraji ta Kasa (FIRS) da Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS).
- CBN Ya Raba Lambobin Da Za A Yi Karar Bankunan Da Ba Sa Saka Kudi A ATM
- An Gudanar Da Dandalin Tattaunawa Tsakanin Kafofin Watsa Labarai Na Bidiyo Na Kasa Da Kasa Karo Na 12 A Birnin Quanzhou
NITDA ta yaba wa kamfanonin kan bin Dokar Aiki A Kafafen Sadarwar Zamani, wadda aka kirkira domin kare masu amfani da kafafen da kuma hana yaduwar abubuwan da ke da illa.
Hukumar ta kuma bayyana cewa wannan doka ta taimaka wajen kara samun kudaden shiga gs gwamnati da kuma inganta matakan tsaro.
NITDA ta yi kira ga hadin kai da ci gaba da kirkiro sabbin hanyoyin magance matsaloli domin tabbatar da yanayin da ya dace a kafafen sada zumunta.