Jama’a barkanku da wannan rana ta juma’a, barkanku da kasancewa tare da wannan shafi na GORON JUMA’A, shafin da yake bawa kowa damar miƙa saƙon gaishe-gaishensa zuwa ga ƴ an’uwa da abokan arziƙi, na kusa da na nesa, har ma da waɗanda aka daɗe ba a haɗu ba.
Kamar kowane mako yau ma shafin na tafe da wasu saƙonnin gaishe-gaishen da ku ka aiko mana, inda saƙon farko ya fara da cewa:
- Jagororin Kamfanonin Ketare Sun Nuna Gamsuwa Dangane Da Zuba Jari A Kasar Sin
- 2027: Jagororin APC Na Kudu-maso-Yamma Sun Amince Da Tinubu Ya Sake Tsayawa Takara
Saƙo daga Fatima Mustapha Hashim, Jihar Zamfara:
Ina gaishe da Mama na da Baffana, sai yayata dake garin Maiduguri wato Yaya Hajiya, sai Yaya Mu’azu da yake karatu a Katsina. Sai ƙawayena na makaranta Suwaibah Muhammad, Hajara, Zauwariyya, Zaina Abdulmajeed, Rukayya Abdullahi, Kausar Nuhu, Fatima Suleiman, Aisha Hafizu, da dai sauransu. Da fatan sun yi juma’a lafiyya, Amin.
Saƙo daga Maimunatu Aliyu, Minjibir Jihar Kano:
Ina gaida Mahaifiyata da Mahaifina, Hajiya Saratu da Alhaji Aliyu Minjibir. Sai Gidana Alhaji Musa Yusuf, sai aminiyata Hajiya Kubra Bashir Abdullahi, sai Ƴa ta Mariya, da ƙannena Rashida Aliyu Minjibir, Zainab Aliyu Minjibir, Aliya Aliyu Minjibir, Aliyu Aliyu, Abubakar Aliyu Minjibir Muhammad Aliyu Minjibir, da fatan sun yi juma’a lafiya.
Saƙo daga Maryam M. Aminu
Saƙon gaisuwata zuwa ga Babata da Babana, sai ƙawayena kamar su; Nawal, Zee-zee Kwalale, Halima Saleh, Fatima Kabir, Maryam Isma’il (Namesake), Keleri. Sannan ƴ an’uwana Yaya, Muhammad, Iman, Al-Amin(TK), Ummulkhurthum, Jawad, Zainab Aminu, Abba, Abdulrahman, Jawahir, Fatima.
Saƙo daga Muhammad Abdullah, Unguwar Fagge Jihar Kano:
Ina gaishe da mahaifiyata da mahaifina dan ba zan fara ba sai na fara da su, sannan ina gaishe da ƴ ar’uwata rabin rai, sai abokaina, da ƴ an’uwan mahaifiyata da ƴ an’uwan mahaifina, da abokaina Aliyu, Aliyu A., Sultan, Ahmad Ghali, Amir, Iman, Ummussalama Abdulrasheed, Hajiya, Siyama, Usman Nasir, Abdulrahman Abdulrashid, Abdulsamad Abdullahi, da atan sun yi juma’a lafiya.
Saƙo daga Chef Maryam (C.E.O Meerah’s Culinary Art Bakery), daga Jihar Kano:
Saƙon gaisuwa ta musamman ga ƴ an’uwana musulmi na faɗin duniya. Sannan ina gaida iyayena sai ɗalibaina, ƙawayena da abokan aikina, kamar su; Fatima Jamilu (Nahnah’s Kitchen), Aisha Kamaluddeen (Princess Ayesha), Rukayya Muhammad Isah, Serah Johnson, Khadija Abdulhadi (Chef Dija/Dijah local Candies), Umaima Sani, Wasila Bello Umar, Dr. Hauwa Aliyu Kaita, Nr. Mrs. Fa’iza Uthman, Nafisa Omar Yahaya (Chef Omson), Dt. Maryam, Ms. Esther Samuel, Dr. Sanaya, Salma M. Rahim, Fauziyya Bukar (Fabz Delight), Asiya Khalil, Dr. Maryam A. A. Phd., Ed. Muhammad Al-amin, Kubra Auwal Yakub (African spices by Chef Hadizat), Hajiya Aisha Jabi, Halima Muhammad Dikko, Acnt. Zakiyya Habib da sauransu. Da fatan suna nan lafiya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp