Jama’a barkanku da kasancewa tare da wannan shafi na Goron Juma’a, da fatan kowa zai yi juma’a lafiya.
Kamar kowanne mako wannan shafi na karato wasikun masu karatu wanda kuka aiko zuwa ga ‘yan uwa da abokan arziki, na kusa dana nesa. A yau ma shafin na tafe da wasu sakonnin gaishe-gaishen naku kamar haka:
- Tinubu Ga Peter Obi: Ka Gargaɗi Magoya Bayanka Kan Ɓata Min Suna
- Tsohon Shugaban Hukumar Binciken Sararin Samaniya Ta Kasa NARSDA, Ya Rasu
Sako daga Shamsiya Adam Jihar Kebbi:
Da farko ina gaida gaida iyayena, ina yi musu barka da Juma’a, sannan ina gaida babban yayana da kannena kamar su Hamida, Suleman, Aliyu, Amina, Rahma, Sadiya, Amatu, A’isha, Khadija, da Anty Zuwaira. Sai kawayena kamar su; Jamila, Fauziyyah, Hafsa, Zainab, Fati da fatan sun yi juma’a lafiya.
Sako daga kueen Nasmah Jihar Zamfara:
Assalamu alaikum, Wannan gaisuwar ta musamman ce zuwa gare ka ‘MAH JAAN (AFTER LIFE OF MINE )’ ina maka fatan Alkhairi, ubangiji ya dafa maka kamar ko yaushe, ubangiji Allah ya sada ka da duka alkhairan duniya , ina fatan yadda ka ga juma’a yau , Allah ya nuna mana ta gabanta da alkhairi Mai Darajata.
Sako daga Hadi Tsohon Sarki Daura-08164205067-08127909054:
Assalamu alaikum. Gaisuwar Goron Juma’a ga Alhaji Ibrahim Bida City, da Muh Idiris Abuja, Alhaji Jinjiri Mile 12 Legas da Shugaba Ahmad Namalan Kazode, da Abubakar Yusuf Zarl Abdullahi Umar da Fadila Lamido da Mujittaba Ya’u, da fatan za su yi Juma’a lafiya, Allah Ya sa haka amin.
Ina kuma mika gaisuwar Goron Juma’a ga Murtala Cd Badarawa Kaduna, Hajara Usman Shuaibu Badarawa Kaduna, Ahmad Mustapha Kwasau, Muhd Kalifa Kano, Binta Dalhatu Kano, Engr Isma’Il Muhd, Hussy Saniey, Ibrahim Danmulky, Lubabatu Auta Ingawa, Zahara’u Abubakar, Muhd Kabeer Kamji da Hafsatu Yusuf da Abdullahi Muhd Kano da sauran ‘yan’uwa musulmi baki daya.