Jama’a barkanku da kasancewa tare da shafin Goron Juma’a, shafin da ke bawa kowa damar mika sakon gaishe-gaishensa zuwa ga ‘yan uwa da abokan arziki, na kusa dana nesa. Kamar kowanne mako shafin na dauke da sakon gaishe-gaihsenku wanda ku ka aiko mana, sai dai za mu tsakuri kadan daga ciki, inda sakon ya fara da cewa:
Sakon daga Rukayya Ibrahim Lawal:
Ina mika sakon gaisuwata ga daukacin ma’aikatan Rmchausatime, da kawata Rahma Sabo Usman, da Mahmood Salis Imam duk ina fatan sun yi sallar jumu’a lafiya.
Sako daga Abdul’aziz Lawan Karkasara Jihar Kano:
Sakon gaisuwa ta zuwa ga mahaifana Hajiya Maryama da Alhaji Lawan Karkasara, da fatan za su yi juma’a lafiya. Ina gaida sauran ‘yan uwana da abokaina kamar su; Hashim, da Khalid, da Yusuf, da ibrahim da sauran wadanda ban ambata ba. Ina gaida masoyiyata abar kaunata mai sunan Mumi na Maryam Shaktey da fatan za ta yi sallar juma’a lafiya.
Sako daga G. Tahir (Yaro da kudi) Jihar Kaduna:
Gaisuwar juma’a ga dan majiya kowa nasa ne, da Happy boy mai kyalkyali, ina gaida yaron Baba dan Hassan, da Musa jiki duk tsoka, ina gaida Hamdiya ‘yar Sarari, da China boy da sauran abokai na, a yi sallar juma’a lafiya.
Sako daga Ibrahim Muhd Abuja Nijeriya:
Ina gaida iyayena, ina gaida ‘yan uwana, da abokaina, da yayyena, da kannena, ina gaida dukkanin musulmin duniya wanda na sani da wanda ban sani ba, da fatan kowa zai yi sallar juma’a lafiay.