Jama’a barkan ku da kasancewa tare da wannan shafi na GORON JUMA’A, shafin da ke ba wa kowa damar mika sakon gaishe-gaishensa zuwa ga ‘yan uwa da abokan arziki, na kusa da na nesa. Kamar kowanne mako, yau ma shafin na tafe da wasu sakonnin gaishe-gaishen, inda kuma muke ba wa wadanda suka turo sakonninsu ba su gani ba hakuri, in sha Allah sakonninku na tafe a wannan shafi. Ga kuma kadan daga cikin sakonnin da kuka aiko mana kamar haka:
Sako Daga Rahma Ibrahim, Jihar Kaduna:
Ina gaida kawayena Salma Ahmad, Zainab Haruna, Maimuna Usman, Maryam Isyaku, Suwaiba Idris, Aisha Ibrahim, Fauziyya Ibrahim, Mariya Hassan, Salma Salisu, Hafiza Yunusa, Mubaraka Auwal, Walida Sa’id, Sannan ina gaida iyayena da sauran ‘yan uwana na gida da fatan za su yi juma’a lafiya.
Sako Daga Muhammad Usman, Jihar Katsina:
Ina gaida babban abokina Irfan Sale, da sauran abokaina kamar su; Ahmad Idris, Yunusa Ibrahim, Habibu Hassan (H2), Tasi’u Muhammad, Bigi dan borno, Habibu Asha Kala, Nasiru Yaro sai da kudi, da masoyiyata abar kaunata Zainab Zee-zee, da mahaifana, da kannena da yayyena, da fatan za su yi juma’a lafiya.
Sako Daga Hajiya Mardiyya Sale Ahmad, Jihar Katsina:
Assalamu Alaikum, sakon barka da juma’a zuwa ga ma’aikatan gidan jaridar Leadership, musamman me gabatar da wannan shafi Rabi’at Sidi Bala, da kuma sauran ma’aikatan kuna burge ni, Allah ya sa ku fi haka, ya kuma kare ku daga sharrin masu sharri, ya kara daukaka gidan jaridar leadership Hausa a duniya. Ina gaida yarana Sa’adu, da fauziyya, da Al’amin, da Sumayya, da Faisal da kuma maigidana Alhaji M’azzam Idi Yari. Allah ya sa a saka mun sakona.
Sako Daga Hafsatu Adam, Jihar Kaduna:
Dan Allah jaridar Leadership a mikan sakon gaisuwata zuwa ga kawata rabin raina Fatima Isah, da kuma Aisha Lawan, da Suwaiba Abdulmuminu, da Sa’adatu Sale, da ‘yan group din “Wanted Girls’ irin su; Lily Girl, Zuly (Ba kida tsoro), da sauran na ciki kowa da kowa. Sai kuma gaisuwa zuwa ga Idris Saminu (Dan Baba), da yayana Kabir Adam, da kanwata Amina Adam, da karamar kanwarmu Safiyya Adam, da kuma Mamana Hajiya Atine Wada, da Abbana Alhaji Adam Maigadaje.
Sako Daga Shafa’atu Tijjani, Karamar Hukumar Rano, Jihar Kano Rano:
Assalamu Alaikum Leadership, na turo sako sau uku ba a saka mun ba, dan Allah a gaishe mun da masoyina wanda zan aura nan ba dadewa Umar Hamza (Asasanta), ina gaishe shi, da kawayena Umaima Sulaiman da Bilkisu Ibrahim, da Zarah Abubakar da Aisha Hamza da sauran kawayena na islamiya dana boko, Allah ya sa za su yi juma’a lafiya.
Sako daga Abdurrahman Tijjani:
Assalaikum alaikum!
Al’umar musulmi baki daya, ina yiwa kowa fatan alkhairi tare da fatan anyi sallar juma’a lafiya Allah ya maimaita mana. Ina gaida iyaye na mamana da babana ina musu fatan alkhairi da fatan sunyi sallar juma’a lafiya Allah ya maimaita mana. Sannan kuma ina gaida ‘yan uwana yayuna da kanne na da fatan sunyi sallar juma’a lafiya. Ina gaida kannan mamana da kannan babana tare da yi musu fatan anyi sallar juma’a lafiya. Sannan ina gaida ‘yan uwa da abokan arziki da fatan kowa yana cikin koshin lafiya tare da barka da juma’a.
Sako daga Safiyya Idris Aliyu Daudawa
Assalamu alaikum ya aka ji da aikin ibada to Allah ya bamu ikon yin ayyukan ibada da za su lunlunka wadanda muka yi kafin a fara Azumin watan Ramadan, ina fatan za a yi sallar Jmumma’a lafiya ita ma babbar ranar ce tare da fatan za a yin sallar Jumma’a lafiya adawo lafiya.
Ina gaida dukkan kawayena wadanda muke makarantar Boko da ta Islamiyya tare,tare da mahaifiya ta da mahaifina, sai ‘yan’uwana da suka hada da Sulaiman, Muhammadu, Fatima, Aisha, Habibu da aka fi sani da suna Khalifa da ‘yar autarmu Nana Hauwa’u.