Jama’a barkan mu da Juma’a, barkanku da kasancewa tare da wannan shafi na Goron Juma’a. Shafin da ke ba wa kowa damar mika sakon gaishe-gashensa zuwa ga ‘yan uwa da abokan arziki na kusa, da na nesa. A yau ma ina dauke da wasu sakonnin gashe-gashen, sai dai kuma kafin na je ga sakonnin masu karatu da suka aiko, sai na fara da mika tawa gaisuwar zuwa ga dukkannin ma’aikatan wannan jarida mai albarka ta LEADERSHIP Hausa, musamman ma Editana Abdulrazak Yahuza Jere, da fatan an yi Sallar Juma’a lafiya, kuma da fatan an yi kwalliyar Juma’a tare da kai ziyara lafiya. Sai sakonnin da kuka aiko kamar haka.
Sako daga Hasan Tijjani:
Assalaikum alaikum. Al’ummar Musulmi, ina yi wa kowa fatan alkhairi tare da fatan an yi Sallar Juma’a lafiya Allah ya maimaita mana. Ina gaida iyayena ina yi musu fatan alkhairi da fatan sunyi Sallar Juma’a lafiya Allah ya maimaita mana. Sannan kuma ina gaida ‘yan uwana yayu na da kanne na da fatan sunyi Sallar Juma’a lafiya. Ina gaida yayye iyaye da kannensu tare da yi musu fatan an yi Sallar Juma’a lafiya. Sannan ina gaida ‘yan uwa da abokan arziki da fatan kowa yana cikin koshin lafiya tare da barka da Juma’a.
Sako daga Isah Aliyu
Ina mika sakon goron Juma’a ga al’umman Musulmi gaba ki daya, da jamia’an tsaro dake kasar nan baki daya. Ina mika gaisuwa na ga mahaifiyata Hajiya Lamee Musa, da mahaifina Alhaji Aliyu Isah. Ina mika sakon gaisuwata ga yayata Ummi, da kanwata Aisha, da yayana Faisal, da kanina Abdulrahman, da yayana Sadik. Da fatan sakona ya iso ku cikin koshin Lafiya.
Sako Daga Yahaya Mai Kaza Kajiji, Legas
Assalama’alaikum LEADERSHIP Hausa, muna masu mika matukar godiyar a gare ku bisa ga irin kokari da kuke yi. Ina son a sake bani dama domin in gaida tsohon chairman na kasuwar ‘yan doya mile12 da Honorable Altine Shehu Kajiji da Honorable Alhaja Mai Dawa Kajiji da Sarkin Hausawan Maryland, Alhj Ali Asara da Anaruwa Mai Kaji Maryland da Basiru Dan Haule a Karshi. Daga karshe ina mika sakon Goron Juma’a ga gagan mai LEADERSHIP Hausa mai kokari ganin ya sada mu da wannan jaridar a kowacce rana wato Malam Tanimu. Muna godiya kwarai.
Sako Daga Fatima Abubakar
Ina mika sakon gaisuwata zuwa ga mijina, ina mika sakon gaisuwata zuwa ga iyayena da fatan alkhairi ina mika sakon gaisuwa zuwa ga ‘ya’yana da ‘yan uwa da abokan arziki na gida da na waje da fatan sun yi Sallar Juma’a lafiya, ina mika sakon gaisuwa zuwa ga daukacin Musulmi tare da fatan an yi Sallar Juma’a lafiya Allah ya maimaita mana amin ya Allah.
Sako Daga Abdulmuminu Sani, Katsina.
Assalamu alaikun. Fatan alkairi ga LEADERSHIP Hausa, ina mai farin cikin da wannan fali namu da aka bamu dama domin mu sada zumunci ga ‘yan’uwa da abokan arziki. Allah ya daukaki wannan Jarida mai farin jini a Duniya baki daya. Ina so in mika sakon gaisuwar Joron Juma’a ga, manyan abokan karatuna kamar su Tasi’u Sirajo (Barrister), da Yunus Abubakar, tare da Rabi’u Abdullahi (baban Tahir), sai kuma Haruna Ibrahim (Baba), da Zakariyya Umar Wade, daga karshe ina mika sakon gaisuwar Goron Juma’a ga Aliyu Muhammad. Da fatan duk suna nan cikin koshin lafiya, Allah ya sa haka, amin summa amin. Barka da Juma’a. 08135391867
Sako daga Bilkisu Maharazu
Assalamu alaikum! Ina mika sakon gaisuwa ga ma’aikatan wannan gidan jarida na LEADERSHIP Hausa tare da mika godiya ta da suka bani damar da na mika sakon gasuwata na gode.
Ina mika sakon gaisuwa ta ga mijina da iyaye na ina fatan sun yi Sallar Juma’a lafiya, ina mika sakon gaisuwa ta ga ‘yan uwana yayye da kannena da fatan suna cikin koshin lafiya sun yi Sallar Juma’a lafiya Allah ya maimaita mana.