Jama’a barkanku da kasancewa tare da shafin Goron Juma’a, shafin dake bawa kowa damar mika sakon gaishe-gaishensa zuwa ga ‘yan’uwa da abokan arziki, na kusa dana nesa har ma da wadanda aka dade ba a hadu da su ba.
Kamar kowane mako yau ma shafin na tafe da wasu sakonnin gaishe-gaishenku da ku ka aiko mana, inda sakon farko ya fara da cewa:
- Gwamna Lawal Ya Yi Jimamin Rasuwar ÆŠan Majalisar Zamfara, Aminu K/Daji
- Jami’an Tsaro Sun Ceto Mutane 10, Sun Kashe Ɗan Bindiga 1 A Katsina
Sako daga Fatima Ishak Jihar Kaduna:
Ina mika sakon barka da sallah zuwa ga iyayena sai ‘yan’uwana Yaya Khadija, Yaya Hauwa’u, Yaya Farida, Yaya Shafa, Yahya Shafi’u, da kawayena, Maimuna, Ruky black, Samira Kabir, Zainab Isah, Hannatu Abubakar, da fatan sun yi juma’a lafiyya.
Sako daga Amina Abdulkudus Jihar Kano:Â
Ina yi wa daujacin jama’ar musulmai na wannan gari, kasa, da ma duniya baki daya barka da sallah a ciki kuwa zan gaishe da Mamana da Babana , sannan Sadiya Rimi, Islam, Nawwara, Khairat, Rahma Abdullahi, Faddima, Mufida, Huda, Labiba, Shamsiyya Adam da fatan sun yi juma’a lafiya kuma sun yi sallah lafiya.
Sako daga Jamilu Usman Jihar Zamfara:
Ina gaida Matata kuma uwargidana Nana Amina da Amarya ta Halimatussadiya da ‘ya’yan Usman, Zahrah, Nana, Jidda, Hanan, Amirah, Hamza, Alida sun yi juma’a lafiya.
Sako daga Wasila Muhammad Jihar Jigawa karamar Hukumar Gumel:
Ina gaishe da Mahaifiyata da Mahaifina na, da kawayena Fiddausi Sa’id Danjuma, Shahida, Walida, Zeenat, Baturiyya, Lawisa da fatan sun yi sallar juma’a lafiya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp