A yayin da muke yaba wa rundunonin tsaro ta bangaren gwamnati da na masu zaman kansu da suke aiki babbu kakkautawa don samar mana da cikakken tsaro tare da tabbatar da al’umma basu fuskantar wata matsala a sassan Nijeriya, muna yaba wa kungiyar maharba mata ta Jihar Taraba, wadda a ‘yan kwanakin nan ta nuna cewa, yaki da rashin tsaro ba abu ba ne da za a kebewa maza kawai suma mata na iya bayar da nasu gudunmawar.
Wadannan jaruman matan sun shiga kafada da kafada wajen yaki da ‘yan ta’addan da suka addabi al’umma jihar a ‘yan shekarun nan.
A Nijeriya tarihi ya nuna cewa, mata sun bayar da gaggarumar gudummawa wajen tabbatar da cikakken tsaro a cikin al’umma kuma bai kamata a manta gaba daya da hakan ba. Haka kuma mata na ci gaba da kasancewa a kan gaba a rundunonin tsaron Nijeriya, kamar Rundunar Sojin Nijeriya, ‘Yan sanda ‘Civil Defense’ da sauran rundunonin tsaro masu zaman kansu wajen yaki da matsalar tsaro a sassan kasar nan.
A kasar da mata suka kai fiye da mutum miliyan 200 wannan ba zai taba zama abin mamaki ga kowa ba. Tabbas rashin sanya mata a cikin tsarin jami’an tsaron kasa ba zai haifar da da mai ido ba musamman ganin yadda matsalar tsaro take kara karuwa.
A ‘yan kwanakin nan wasu jaruman mata suka hada hannu da takwarorin su maza a Jihar Taraba, don su yaki ayyukan ta’addanci da ta addabi yankunan, a halin yanzu zawarawan da ‘yan mata suna gangamin shiga wannan kungiyar, wannan wani lamari ne da ya kamata a yaba a kuma karfafa. Hare-haren da ake kai wa mata da yara kanana ya tilastawa matan shiga wannan kungiyar tare da daukar makamai don kare al’ummar su.
Idan za a iya tunawa a watan Janairu na shekarar 2022 ne aka tura akalla sojoji mata fiye da 300 don aiki tare da sauran jami’an tsaron wajen yaki da ayyukan ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane da sauran ayyukan ta’addanci a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja a daidai lokacin lokacin da lamarin ayyukan ta’addancin ya ta’azzara.
Hakanan ma a shekarar 2018, shugaban rundunar sojojin Nijeriya na wancan lokacin Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai, ya karfafa mata yayin da ya kafa wata runduna ta musamman a yankin Afirika ta yamma.
Shigar da mata cikin tsarin harkar samar da tsaro a dukkan matakai a Nijeriya abu ne da ya karbu a sassan duniya kuma bai kamata a ce Nijeriya bata shiga sahu ba.
A lokacin da Buratai ya kafa Rundunar Sojoji Mata na Sojojin Nijeriya, ya bayyana cewa, “Za a ba rundunar dukkan goyon bayan da take bukata na shigar da mata a tsaron don su bayar da gudummawarsu na tabbatar da cikakkiyar tsaro a kasar mu.
Tarihi ya nuna irin nasarorin da mata suka samu a kokrin samar da tsaro a sassa daban-daban a Nijeriya. A wannan fannin tabass za mu iya tuna kungiyar tsaro da ake kira ‘Female amazons’ ta Jihar Filato, wadanda suke saukowa daga kan tsaunuka don kare al’ummar su daga hare-hare, haka kuma muna iya tunawa da Sarauniya Amina wadda ta jagoranci dakarun mahaifinta a yake-yake da aka yi wajen kare daular Zazzau.
Akwai kuma wasu mayaka mata a wasu kasashen yankin Afirka ta Yamma da suka hada da kasar Dahomey, a wanncan lokacin ana kiran matan da sunan “Black Sparta.” Sun yi kokarin fafatawa ba tare da tsoro ba wajen tunkarar yakin da ake yi da safarar mutane da sunan bayi.
Jarumai mata a sassan duniya sun nuna cewa, mata na iya bayar da gudummawar su wajen yaki da matsalar tsaro tare da tabbatar da tsaro a cikin al’umma.
An kuma samu rahotannin zaratan sojoji mata da suka fafata a cikin dakarun kasar ‘Kurdish Peshmerga’ a watan Yuni na shekarar 2014, inda suka shiga sahun dakarun da suka yaki don kwato garin Mosul na kasar Irak daga hannun kungiyar nan ta ‘yan ta’adda ta ISIS. Haka kuma bayan shekara 2 sun kuma kara fafatawa a karkashin dakaru mata fiye da 1,000 inda suka ceto garin Kirkuk da wasu rijiyoyin mai na kasar Irak daga hannun ‘yan ta’addar kungiyar ISIS.
A al’adance ana ganin mata a mastayin masu rauni da ba za su iya tafiya kafada da kafada da takwarorinsu maza ba amma a halihn yanzu al’amurra sun canza, yanzu mata na hada hannu da maza wajen dukkan ayyukan samar da tsaro a cikin al’umma.
A jawabin Gwamnan Jihar Kaduna a yayin da yake karbar matan da aka turo don yin aikin samar da tsrao a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja, ya ce, “tabbas duk abin da namiji zai iya yi mace ma za ta iya yin fiye da haka. Mun yi imanin matan Jihar Kaduna suna iya gabatar da ayyuka kamar maza suna kuma da kwarewar da ake bukata, za mu baku dukkan gudummawar da ake bukata don ku samu nasarar da ake bukata a wanan lokacin, muna alfahari da kasancewa ku, zuwan ku zai karfafa sauran matan jihar shiga aikin soja,” In ji shi.
Ba zamu manta da ‘Flying Officer Tolulope Arotile, da gudummawarta ga yaki da ta’addanci a yankin arewacin Nijeriya ba. Ita ce mace ta farko da ta fara tuka jirgin saman yaki na rundunar sojojin sama a Nijeriya. Nijeriya ta yi alhinin rasuwarta a shekarar 2021.
Haka kuma muna tuna mata da dama da suka rasa rayukansu ko suka bace a yayin da suke bautawa kasar haihuwarsu. Za a ci gaba da tunawa da su har abada.