Burin dukkanin bil adama ne samun kyakkyawar rayuwa, da muhalli mai tsafta da kyan gani, mai ruwa garai-garai, da tsaunuka masu kayatarwa, da muhallin halittu mai ni’ima, wato dai muhallin da dan adam da sauran halittun dake kewaye da shi ke zaune cikin lumana da juna.
Yayin da nake kara samun zarafin ziyartar sassan kasar Sin daban daban, ina kara ganin wasu manufofi da mahukuntan kasar ke aiwatarwa, ta fuskar daidaita zaman rayuwar bil adama da sassan halittu, da muhallin dake kewaye da shi, tare da hada gwiwa da sauran kasashen duniya wajen gina duniya mai tsafta da kyan gani.
- Dokar Haraji Za Ta Ƙara Jefa Al’umma Cikin Talauci – Gwamnatin Kano
- Gwamnatin Kano Ta Yi Fatali Da Kudirin Sake Fasalin Dokar Haraji
Salon zamanantarwa na Sin na kunshe da manufar zaman jituwa tsakanin mutane da halittun dake kewaye da su. A halin da ake ciki, kasar Sin na ci gaba da samun manyan nasarori a fagen bunkasa kasa ba tare da gurbata muhalli ba. A daya hannun kasar Sin na ta kara raba dabarunta na kyautata muhalli tare da sauran sassan kasa da kasa.
Karkashin hakan, kasar Sin na aiwatar da manufofi da suka hada da kafa ginshikin zamanantarwa irin ta Sin, da hada gwiwa da sauran sassa wajen ingiza burin samar da ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, da kuma goyon bayan jagorancin inganta muhalli a matakin kasa da kasa, ta yadda za a gudu tare a tsira tare
Kawo yanzu, Sin ta sanya hannu kan takardun fahimtar juna da dama, masu nasaba da hadin gwiwar kyautata yanayi, tare da kasashe masu saurin bunkasa da kasashe masu tasowa, ta kuma fara aiwatar da tarin ayyukan dakile mummunan tasirin yanayi, da samar da juriyar tasirin hakan. Har ila yau, Sin ta dauki nauyin gudanar da tarukan karawa juna sani sama da 300 a fannin dakile sauyin yanayi.
Alal hakika, Sin ta yi imanin cewa daukacin bil adama na da makoma ce ta bai daya, don haka take dagewa tukuru, wajen ba da gudummawar gina duniya mai tsafta da kayatarwa ga kowa.
Shaidun zahiri sun tabbatar da kwazon Sin a fannin ingiza zamanantarwa ta Sin a fannin zaman jituwa tsakanin mutum da halittun da yake rayuwa tare da su, tana kuma himma wajen yaukaka musaya, da hadin gwiwa da sauran sassa a ayyukan kare muhallin halittu, ta yadda daukacin bil adama zai more kyakkyawar rayuwa, da makoma mai haske ta bai daya. (Saminu Alhassan)