Ilimi na matukar bayar da gudunmawa wajen ci gaban al’umma, musamman ma idan ya kasance akwai masu ilimi da dama a cikin al’ummar. Ga dai wasu daga cikin gudunmawar da ilimin ke bayarwa kamar haka:
1. Samar Da Hanyoyin Ayyukan Yi
Samun aikin yi, ba karamin lamari ba ne; musamman a irin halin da ake ciki yanzu na matsalar tattalin arziki da tsadar rayuwa.
Ko shakka babu, yanzu haka ana cikin wani irin yanayi ne na gwagwagwa da daruruwan wadanda suka kammala makaranta, ba tare da samun aiki yi ba.
Haka zalika, abin la’akari a nan shi ne; idan ilimin da ake da shi ba wani mai zurfi ba ne, za a iya samun mutane da yawa da suke neman aiki.
Amma, idan kuma ilimin mai zurfi ne, wato kamar makarantar gaba da Sakandire, ilimin da aka fi so da yadda aka fara yin sa, akwai yiwuwar samun aiki; ba sai an wani bata lokaci ba, sannan za a iya samun albashi mai tsoka.
Don haka, idan har kana bukatar kasancewa cikin wadanda za a rika yin wawarsu, sakamakon tsayawa da suka yi suka jajirce wajen yin karatu, wajibi ne kai ma ka mayar da hankali a makaranta har sai ka cimma naka burin na karatu.
2. Samun Kudade Ta Hanyoyi Daban-daban
Wadanda suka tsaya suka yi karatu a makarantun gaba da Sakandire tare da samun kwarewa a fannoni daban-daban, na daya daga cikin wadanda za su samu aikin yi; ba tare da shan wuya ba, domin kuwa har daga kasashen waje za a rika rubibin su.
Don haka, A yi kokari wajen yin wannan karatu yadda ya dace tare da samar da lokaci; domin samun irin ilimin da ake bukata, irin haka ne ke sa wa a samu rayuwa mai inganci; wadda kowa da kowa zai yi sha’awar kasancewa cikinta.
Takardunka ko satifiket daban-daban da ka samu, su ne za su yi bayanin ko kai wane ne, su ne kuma za su ja hankalin masu daukar ka aiki. Saboda haka, lallai a yi karatu tukuru a makaranta; duk tsawon lokaci ko shekarun da za a dauka kafin a gama.
Kazalika, ta hanyar duba wannan satifiket ne, masu daukar aiki ke iya gane, wadanda suka mayar da hankali a karatunsu, suka kuma san abin da suke yi.
3. Samar Da Ilimin Da Za A Yi Maganin Wasu Matsaloli
Daya daga cikin muhimmancin ilimi shi ne, koya mana yadda za mu samu ilimi tare da yin amfani da shi wajen yin tunani, domin daukar matakin da zai taimaka mana a rayuwarmu.
Kamar yadda aka sani ne, bayan yara sun kammala karatunsu sun samu aiki yi, nauyi tare da matsaloli na hawa kansu ta fuskoki da dama, da farko dai yadda za su biya bashin da suka karba a lokacin sa suna makaranta da yadda za su mallaki gida ko mahalli da kokarin sayen mota da kuma biya wa iyali nasu bukatun da dai sauran makamantansu.
Koda-yake, mutane da dama na shafe shekara da shekaru wajen gwagwarmayar neman wannan ilimi, duk da hakan ya dace a ce suna iya daukar mataki dangane da wasu al’amura nasu. Amma, abin bai tsaya kadai a nan ba, domin kuwa akwai bukatar har sai idan har sun kai ga samun mafita kan matakan da suka dauka; domin samun ingantacciyar rayuwa da kuma ci gaba.
4. Bunkasa Tattalin Arziki
Mafi yawan lokuta, mutanen da suka samu ilimi mai zurfi da nagarta, sun fi samun ayyukan da ake biyan albashi mai tsoka, yadda mutum ya mallaki takardu ko satifiket na ilimi mai zurfi da muhimmanci, irin hakan ne ke bayar da damar samun aiki mai nagarta, inda za a rika ba da albashi mai matukar tsoka.
Har ila yau, ilimi na taimaka wa kasashe wajen samun bunkasa da ci gaban tattalin arziki, sakamakon ilimin da Allah yah ore musu tare da sanin hanyoyin da za su sarrafa shi da kuma yin amfani da shi yadda ya kamata, musamman wajen bunkasa rayuwar al’ummarsu.