An ɗage wasa tsakanin Everton da Liverpool wanda ake wa lakabi da Merseyside derby a filin wasa na Goodison Park saboda rashin kyawun yanayi inda aka samu iska mai ƙarfi wanda ake kira Storm Darragh ya haddasa.
Hukumomi sun ba da gargadin iska mai ƙarfi da ka iya shafar wasan a Merseyside wanda aka shirya yi a safiyar ranar Asabar. An ɗage wasan ne bayan wata ganawa da ƙungiyoyin biyu suka yi da wakilai daga ‘yansandan Merseyside da na Liverpool City Council.
- Yadda Arsenal Ta Raba Maki Da Liverpool A Emirates
- Liverpool Ta Sake Nuna Barakar Real Madrid A Anfield
Sanarwar da Everton ta fitar ta ce “Duk da cewa hakan zai zama abin takaici ga magoya baya, da ma’aikata da ‘yan wasa na da matuƙar muhimmanci.”
Liverpool ta ce shawarar ta kasance “saboda haɗarin da ke tattare da tsaro a yankin”.
Tun da farko an shirya fara wasan ne da karfe 12:30 agogon GMT kuma zai kasance wasan ƙarshe na gasar lig tsakanin ƙungiyoyin biyu a Goodison kafin Everton ta koma wani sabon filin wasa a shekarar 2025.
Liverpool ta bai wa Chelsea da Arsenal tazarar maki bakwai a teburin Premier, inda dukkanin ƙungiyoyin biyu za su fafata a ranar Lahadi a Tottenham da Fulham.
An faɗawa miliyoyin mutane a sassan Wales da kudu maso yammacin Ingila da su zauna a gida don guje wa haɗari yayin guguwar.