“Hauka,” “wauta” da “rashin hankali” su ne kalmomin da masharhanta ke amfani da su wajen bayyana ra’ayoyinsu game da matakin kakaba harajin fito da shugaban Amurka Donald Trump ya dauka a ranar da ya yiwa lakabi da “Ranar ‘Yanci,” wato ranar 2 ga Afrilu. Babu abin da ya fi faranta ran Trump sama da ya wayi gari ya ga kansa tsaye a lambunsa na Rose Garden rike da takarda mai dauke da jerin sunayen kasashen da zai kakaba wa sabon haraji a karkashin manufarsa ta “Make American Great Again” wato MAGA a takaice. Bayan sanin kowa ne cewa da yawa daga cikin kasashen da ya kakaba wa sabon harajin fiton kananan kasashe ne da ke rayuwa cikin kangin talauci, don me kasashe kamar su Lesotho, Laos, da Kambodiya za su biya karin kudin fito don kawai Amurka ta wadata? Shin sun ba da gudummawa ga rasa yawancin masana’antun da Amurka ta yi cikin tsawon shekaru ta hanyar manufofin mika masana’antunta da kuma karfinta na kwadago ga kasashe masu arhan kwadago ne? Shin wadannan al’ummomi ne ke da alhakin durkushewar biranen Amurka har suka zama tamkar yankin marasa galihu, da yankunan masana’antu na Amurka da suka zama kamar kufai? Mene ne laifin gungun bakarariyar tsibiri, da dutse mai aman wuta da ke kusa da Antarctica, wanda ke lullube da dusar kankara dake zama gida ga dabbobin Penguin da ya laftawa harajin fito kashi 10 cikin dari, me za mu kira wannan in ba hauka ba?
Manufar harajin Trump ba wani abu ba ne illa yunkurin sanya kasashen duniya samar da kudaden da zai yi amfani da su wajen farfado da tattalin arzikin Amurka. Daular Birtaniya ta aiwatar da irin wannan manufar a karni na 19 lokacin da ta azurta ’yan jarin hujja na Birtaniya yayin da ta tatse dukiyar Afirka da Asiya ta hanyar mulkin mallaka. Ganin cewa barazanar ta riga ta tayar da kura a kasuwannin duniya, lamarin da ya tilastawa Trump kira da a dakatar da matakin na tsawon kwanaki 90 kafin aiwatar da shi, wato a kan dukkan sauran kasashe amma ban da kasar Sin, wanda daga bisani ya laftawa karin harajin fito kashi 145 cikin dari. Masharhanta na ganin togaice kasar Sin da Trump ya yi wani yunkuri ne rage rawar da kasar Sin ke takawa a duniya musamman a hadin gwiwarta da kasashe masu tasowa karkashin shawarar “Ziri daya da Hanya daya”, saboda a ganinsa gurgunta tattalin arziki Sin zai kawo koma baya ga kasashe masu tasowa ta yadda za su dawo su rusuna gaban Amurka don neman mafita. Da yawa daga cikin wadannan kasashe masu tasowa sun san wannan gaskiyar. Yayin da za su dan numfasa tsawon kwanaki 90 kafin tsarin harajin fiton ya sake rike musu wuya, sun san wanene abokinsu kuma wanene makiyinsu.
Idan akwai wata hanyar magance wannan haukar, to tana iya zama mai ban mamaki, saboda a tarihin Amurka na manufofin neman sassaucin ra’ayi tun daga shekarar 1980, tsarin biyan haraji na Amurka ya zama mafi cutarwa, wanda ke dora kason haraji mafi girma kan Amurkawa talakawa da kananan ma’aikata tare da dora mafi kankantar haraji kan masu arziki. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp