A kasar Indonesia, wadda ta fi kowace kasa yawan Musulmai a Duniya, an samu wata zanga-zangar mutane akan wani gunkin da mutanen kasar China da ke zaune a kasar suka sassaka, gunkin wanda aka kashe kudi sama da miliyan casa’in (a kudin Nijeriya) wajen yin sa kuma aka ce shi ne mafi girma a gaba dayan kudancin yankin Asia, yana ci wa Musulman Kasar Indonesian rai, ganin cewa kasar ta Musulmi ce, wannan ya sa suka fito suka nuna fushinsu sannan suka bukaci da a lalatashi.
Zanga-zangar tasa dole aka rufe wannan gunkin da farin kyalle, saboda a samu kwanciyar hankali, sai dai babu tabbacin ko za’a lalata gunkin kamar yadda masu zanga-zangar suka bukata.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp