MDD ta gabatar da jawabin da babban sakataren MDD António Guterres ya yi, game da murnar sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin a jiya, inda Guterres ya bayyana cewa, a yayin shekarar Loong ta kasar Sin dake tafe, yana mika wa Sinawa gaisuwar sabuwar shekara.
Guterres ya bayyana cewa, shagalin murnar bikin sabuwar shekara na kasar Sin na bana da MDD take yi ya sha bamban da na baya, domin bikin sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin ya shiga jerin sunayen bukukuwan MDD a karo na farko. Ya ce yana mika godiya ga kasar Sin da jama’arta bisa cikakken goyon bayan da suke baiwa MDD da hadin gwiwar bangarori daban daban da bunkasuwar duniya. Ya ce, muddin aka yi kokarin aiki tare, za a iya cimma makoma mai dorewa, adalci da zaman lafiya. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp