Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya nemi afuwa kan garkeme kafafen yada labarai da ya yi a jihar.
Kafafen da lamarin ya shafa sun hada da, NTA, FRCN, Pride FM Gusau, Gamji TV, Gamji FM Al-umma TV da kuma wasu Uku masu zaman kansu.
Gwamnan ya sanar da hakan ne a cikin sanarwar da kwamishinan yada labarai na jihar Ibrahim Dosara ya fitar, inda ya kara da zargin cewa, kafafen yada labaran da abin ya shafa, sun saba doka ta 10 da kuma cin zarafin aikin jarida.
Shi ma wani jigo a APC a jihar, Dakta Abdullahi Shinkafi wanda kuma shine shugaban kwamitin yanke wa ‘yan bindiga hukunci da masu aikata sauran laifuka a taron manema labarai, a jiya Litinin a Gusau ya sanar da cewa, gwamnatin jihar ta harzika ne a kan taka dokarta ta 10 ta shekarar 2022 wacce kuma ta fara aiki a ranar 30 ga watan Oktoban 2022.
Dokar ta 10, ta haramta gudanar da duk wani irin gangamin yakin neman zabe saboda kalubalen rashin tsaro da jihar ke ci gaba da fuskanta.
Ya kara da cewa, haka gwamnatin tuni ta haramta yin gangamin yakin neman zabe a kananan hukumomin Anka, Bukuyum da Gummi da kuma sauran sassan jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp