Kusan yara bakwai daga Jihar Bauchi aka sake hadawa da iyayensuwanda Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir ya jagoranta.Â
Hakan na kunshe cikin jawabin da Daraktan yada labaran Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa , ya raba wa manema labarai a Kano.
- Amfanin Ganyen Magarya Ga Lafiyar Dan’adam
- Tsadar Rayuwa: ‘Yan Nijeriya Na Rungumar Bashin Banki
Gwamnan ya jinjinawa kokarin rundunar ‘yansandan Jihar Kano karkashin jagorancin kwamishinan ‘yansanda Muhammad Hussain Gumel.
Gwamna Yusuf, ya bayyana matukar damuwarsa game da yadda aka tabbatar da cewar wadannan yaran an sato su ne daga Jihar Baichi aka kuma yi fataucin su tare da sayar da su a Jihar Anambara da Jihar Legas.
Don haka sai Gwamnan ya bukaci iyayen yaran da su kara himma wajen lura tare da kulawa da yaran nasu wanda ke zaman abin da ya fi cancanta a kula da su, haka zalika ya bukaci takwararsa Gwamnoni musamman Gwamnan Bauchi da yauki matakin gaggawa domin damke kafatanin wadanda ake zargin.
Da yake gabatar da jawabinsa a madadin iyayen yaran, Malam Sa’ad wanda uba ne ga daya daga cikin yaran da aka sato, Abdulmutallif, ya bayyana farin cikinsa ga Gwamnan na Kano da kuma kwamishinan ‘yansandan Jihar Kano bisa wannan gagarumin aiki.
An damke mutane tara wadanda ake zargin aikata laifin da ‘yansandan Jihar Kano ta yi a tashar motar da ke Mariri alokacin da suke kokarin tserewa da yaran zuwa Jihar Legas.