Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya ce babu wani mutum ko wata kungiya da za ta iya haifar da rashin jituwa tsakaninsa da mai ba shi shawara a harkokin siyasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, inda ya nanata alakarsa da Kwankwaso tana nan daramdam.
Yusuf ya bayyana hakan ne a yayin bikin cikarsa (Kwankwaso) shekaru 69 a duniya a gidansa da ke titin Miller a Kano.
- Gwamnatin Tarayya Ta Jajantawa Waɗanda Fashewar Tankar Mai Ta Rutsa Da Su A Neja
- Shugabannin jam’iyyar PDP Na Arewa Sun Amince Da Turaki A Matsayin Ɗan Takarar Shugabancin Jam’iyyar Na Ƙasa
Gwamnan ya bayyana Kwankwaso, wanda tsohon gwamnan jihar Kano ne sau biyu kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP, a matsayin shugaba mai hangen nesa kuma mai kishin jama’a da ya sadaukar da rayuwarsa ga al’umma.
“Allah ya albarkace mu da shugaba mai tsoron Allah da kishin jama’a – mutum ne mai kaunar al’ummar jihar Kano da Nijeriya, kuma me aiki tukuru domin ganin ci gabansu,” in ji Yusuf.
Ya kuma jaddada kudirin sa na ciyar da jihar gaba bisa tsarin falsafar Kwankwasiyya, wanda ke jaddada hidima, rikon amana, da tallafawa.
A nasa jawabin, Kwankwaso ya bukaci ‘ya’yan jam’iyyar NNPP da na Kwankwasiyya na kasa baki daya da su ci gaba da hada kai da kuma jajircewa wajen ci gaban jam’iyyar.
Ya kuma mika godiyarsa ga shugaban NNPP na kasa Dr. Ajuji Ahmed, da sauran shugabannin jam’iyyar daga jihohi sama da 30, da masu biyayya da suka halarci bikin.