Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya umarci dukkan kwamishinonin da ya sauyawa ma’aikatu su tabbatar an sun miƙa rahotonsu tare da kama aiki a sabbin ma’aikatan da aka sauya musu ba tare da wata matsala ba kafin ranar Talata 17 ga watan Disamba 2024.
Cikin wata sanarwa ta bakin mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa, gwamnan ya bayyana cewa sauye-sauyen majalisar ta sa za su kankama a zamanta na gaba wato ranar Laraba 18 ga watan Disamba 2024.
- Gwamnatin Tarayya Za Ta Raba Wa ‘Yan Nijeriya Mitar Lantarki Miliyan 10 A Farkon 2025
- Adadin Hatsin Da Kasar Sin Ta Samu A Bana Ya Haura Tan Miliyan 700
Ya jaddada buƙatar kammala dukkan ayyukan miƙa rahoton kafin ranar, inda ya yi kira ga dukkan kwamishinonin da sauye-sauyen ya shafa da su miƙa ayyukansu tsakanin ranakun Litinin, 16 ga wata zuwa Talata, 17 ga Disamba, 2024.
Gwamnan ya kuma buƙaci ‘yan majalisar zartaswar jihar da su kara himma tare da tabbatar da haɗin kai da sadaukarwa da ma jajircewa wajen tallafa wa gwamnatinsa na yi wa al’ummar jihar Kano hidima.