Gwamnan Jihar Ondo, Hon. Lucky Aiyedatiwa, ya bai wa ’yar wasan Super Falcons, Tosin Demehin, kyautar Naira miliyan 30 da gida a Sunshine Estate, Oba-Ile, Akure, saboda rawar da ta taka a gasar WAFCON 2024 da Nijeriya ta lashe.
A taron tarɓar ƴan asalin jihar da suka wakilci Nijeriya a gasar da aka gudanar a Maroko, Gwamnan ya bayyana cewa wannan lambar yabo wata hanya ce ta girmamawa ga jajircewa da ƙwarewar Demehin, ’yar asalin ƙaramar hukumar Ilaje.
- Ruwan Wuta Ne Kawai Maganin ‘Yan Ta’adda Ba Sasanci Ba – Mataimakin Gwamnan Zamfara
- Tsauraran Manufofin Tattalin Arziƙin Tinubu Ya Ƙara Yawan Matalauta – Falana
Haka kuma, Gwamna Aiyedatiwa ya bai wa jami’ar hulɗa da manema labarai ta Super Falcons, Mary Akinsola, da sakatariyar ƙungiyar, Mary Oduboku, kyautar Naira miliyan 15 kowaccensu saboda irin gudummawar da suka bayar wajen nasarar tawagar.
Ya ce gwamnatin jihar za ta ci gaba da saka jari a cikin matasa da kuma harkar wasanni don ciyar da su gaba, tare da bayar da tallafi ga ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na jihar da suka haɗa da Sunshine Stars.
Tosin Demehin ta nuna godiya da jin daɗinta, tana mai cewa wannan girmamawa daga jiharta na ƙarfafa mata gwuiwa da sauran ’yan mata masu burin taka leda a matakin duniya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp