Gwamna Ahmed Aliyu na Sokoto ya tsige hakimai 15 daga kan karagar mulki, bisa zarginsu da laifin rashin biyayya, satar filaye, taimakawa harkar ta’addanci, da mayar da kadarorin al’umma zuwa amfanin kashin kai.
Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan, Abubakar Bawa, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya sanyawa hannu kuma ya rabawa manema labarai a ranar Talata.
- Dalilin Haramta Tafiyar Dare A Iyakokinmu Da Katsina Da Sokoto – Gwamnatin Zamfara
- Dalilin Haramta Tafiyar Dare A Iyakokinmu Da Katsina Da Sokoto – Gwamnatin Zamfara
Sanarwar ta ce, wadanda abin ya shafa sun hada da Hakiman Unguwar Lalle, Yabo, Wamakko, Tulluwa, llela, Dogon Daji, Kebbe, Alkammu, da Giyawa.
Bawa yace, sauran shidan su ne wadanda tsohon Gwamna Aminu Tambuwal ya nada.
Ya ce, an sauke su ne saboda tsarin yadda aka nada su bai dace ba, jama’arsu ba su aminta da su ba.
Sun hada da Marafan Tangaza, Sarkin Gabas Kalambaina, Bunun Gongono, Sarkin Kudun Yar Tsakkuwa, Sarkin Tambuwal, da Sarkin Yamman Torankawa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp